Hukumar ta Akkuyu NPP da ke gundumar Gulnar ta Mersin, za ta samar da wutar lantarki mai karfin kilowatt biliyan 35 bayan kammala dukkan rukunan huɗu. Hoto: AA Archive

Turkiyya ta bai wa kamfanin Nukiliya Akkuyu izinin gudanar da na'urar samar da wutar lantarki ta farko ta tashar makamashin nukiliya ta farko a lardin Mersin da ke kudancin kasar.

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Talata ya ce ya gabatar da kashin farko na takardu a ranar 17 ga Maris, na biyu kuma a ranar 24 ga watan Agusta ga hukumar da ke sa ido kan makamashin nukiliya ta Turkiyya don samun izini.

Bayar da izinin ya biyo bayan farawa da daidaita yadda ayyukuan za su tafi da kuma kawo gaɓar matakai na ƙarshe na gina tashar nukiliya don aiki mai aminci.

"Matakin da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Turkiyya ta dauka na ba da izinin kaddamar da rukunin farko na tashar Akkuyu NPP ya tabbatar da cewa mun cika dukkan sharuddan dokokin Turkiyya na kasa da kasa na gina tasoshin nukiliya kuma a shirye muke mu ci gaba," a cewar Anastasia Zoteeva, darakta janar ta kamfanin Akkuyu, kamar yadda aka ambato ta tana faɗa a wata sanarwa da aka wallafa a shafin Telegram.

Matakin na baya-bayan nan, in ji ta, shi ne mafarin "sabon, muhimmin mataki mai muhimmanci na fara aikin," ta ƙara da cewa mataki na gaba shi ne samun lasisin sarrafa na'urar samar da wutar lantarki ta farko.

Hakan zai ba su damar fara lodin makamashin nukiliya a cikin injina da kuma fara gudanar da ayyukan sarrafa man fetur kafin a fara aiki, in ji ta.

Sanarwar ta ƙara da cewa, "A halin yanzu, ƙwararru a fannin Nukiliya na Akkuyu suna ci gaba da samar da bayanan fasaha don neman lasisi."

Hukumar ta Akkuyu NPP da ke gundumar Gulnar ta Mersin, za ta samar da wutar lantarki mai karfin kilowatt biliyan 35 bayan kammala dukkan rukunan huɗu.

Bisa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Turkiyya da Rasha, ana sa ran rukunin farko zai fara samar da wutar lantarki a shekarar 2025, shekaru bakwai bayan samun lasisin gina na'urar samar da wutar lantarki ta farko.

TRT World