Shugaba Erdogan na daga cikin 'yan takarar shugabancin Turkiyya a zaben da ke tafe. Photo/AA

A lokacin zaben Turkiyya wanda za a yi a ranar 14 ga watan Mayu, ‘yan takara hudu ne wadanda suke neman kujerar shugaban kasa da suka hada da shugaba mai ci Recep Tayyip Erdogan da Kemal Kilicdaroglu da Muharrem Ince da kuma Sinan Ogan.

Bisa dukkan alamu, masu zabe akasari za su fi mayar da hankali ne kan halin da tattalin arzikin Turkiyya yake ciki, da kuma ayyukan da sauran ‘yan adawan da kansu ya rabu suka yi.

Sannan akwai yunkurin da ake yi na sake gina yankin da girgizar kasa ta afkawa a kudancin kasar a ranar 6 ga watan Fabrairu.

‘Yan adawa a Turkiyya na ganin cewa halin da tattalin arzikin kasar ke ciki kadai zai iya kawo cikas ga Erdogan wurin samun nasara.

Sai dai Jam’iyyar Justice and Development wato AK wadda shugaban kasar yake na ganin matakan da gwamnati ke dauka kamar karin albashi mai yawa a tsarin karancin albashin kasar na nuna kokarin shugaban na dakile matsalolin tattalin arziki.

Hukumomin Jam’iyyar AK na kara jaddada cewa irin matakan gaggawa da Shugaba Erdogan ya dauka bayan girgizar kasar da aka yi ta kara masa farin jini.

‘Jama’a na neman mafita wurin Erdogan’

Jami'an Jam'iyyar AK sun ce ba za a iya la'akari da matsalolin tattalin arzikin Turkiyya ba, ba tare da duka irin matsalar tattalin arzikin duniya ba, inda suke jaddada cewa ita girgizar kasa bala’i ce da za a iya jarabtar kowace kasa da ita.

A kalaman da Erdogan ya yi, Turkiyya za ta bukaci kusan dala biliyan 104 ne domin farfadowa daga radadin girgizar kasar da aka yi.

Duk da kalubalen da ake fuskanta, mambobin Jam’iyyar AK na da yakinin cewa jama’ar Turkiyya sun gane cewa Erdogan shi ne mutumin da ya dace ya maganace matsalolin da ke tasowa.

Kuri’ar jin ra’ayi da Jam’iyyar AK ta yi ta nuna cewa tun a zagayen farko Shugaba Erdogan zai ci zabe da kashi 54 cikin 100, kamar yadda Osman Nuri Kabaktepe ya bayyana, shugaban Jam’iyyar AK lardin Istanbul.

Daya daga cikin muhimman tambayoyi a kuri’ar jin ra’ayin na da alaka da bala’in da ya faru a ranar 6 ga watan Fabrairu wanda kuma ya zama babban abin tattaunawa ga sauran masu zaman kansu da ke kuri’ar jin ra’ayi.

Dukan su dai sun gano cewa akasarin jama’ar Turkiyya na ganin Erdogan zai iya daukar nauyin farfado da lamura ba wai ‘yan adawa ba musamman ta bangaren gidaje da gine-gine da daukar aiki.

A kuri’ar jin ra’ayin, kwarin gwiwar da jama’a ke da shi kan Erdogan da kuma kokarin da ya yi wurin kula da aikin farfado da yankin girgizar kasa musamman a wurare uku da ta fi shafa, ya kai kashi 70 cikin 100, kamar yadda Kabaktepe ya bayyana.

Mustafa Sen, wani jami’i a Jam’iyyar AK, ya bayyana cewa jama’a sun san cewa za su iya dogara kan Erdogan. “Mutane na ganin matsaloli, haka shi ma Erdogan.

"Ba ya boyewa ko kuma kokarin boye hakan. Mutane na neman mafita ta wurin Erdogan. Sun san cewa zai iya warkar da ciwon da ke zukatan jama’a wadanda girgizar kasa ta jawo,” in ji shi.

“Akwai wani dalili kuma a cikin duka wadannan: ‘yan adawa ba su yi wani abu ba zuwa yanzu. Mutane ba sa ganin wani alheri a tattare da jerin jam’iyyu shidan.”

‘Yan adawa na ta matsa kaimi wurin caccakar matakan da ake dauka game da girgizar kasa, inda suke sukar gwamnatin kan cewa tana tafiyar hawainiya kuma ayyukan ba su tasiri.

A martanin da Erdogan ya mayar kan wannan lamari, ya bayyana cewa gyara yankin da girigizar kasa ta lalata ya zama daya daga cikin muhimman burin gwamnatin kasar.

Duk da cewa zabe na ta matsowa, ya fi mayar da hankali kan wuraren da lamarin ya shafa, inda yake yawan zuwa wurin tare da tabbatar wa jama’ar wurin kan cewa matsalarsu ta fi damunsa fiye da yakin neman zabensa.

Ya sha bayyana cewa cewa ba shakka babu abin da ya fi muhimmanci kamar taimaka wa wadanda suka tsira daga girgizar kasa domin sake gina rayuwarsu da kuma tsayawa a kan kafafunsu.

“Ba tare da la’akari da abin da wasu ke yi ba, ko ma wace irin manufa mara kyau suke da ita, muna shafe kowace rana muna mayar da hankali kan abubuwan da suka danganci girgizar kasa,” kamar yadda Erdogan ya bayyana a wata ziyara ta kwananan da ya kau kudancin Lardin Kilis.

Kuri’a daga kowane bangare

Wani dalili da ake ganin ya sa Erdogan yake da karfi shi ne yadda yake da kuri’u daga masu zabe a fadin Turkiyya da suka fito daga kabilu da addinai daban-daban, kamar yadda Kabaktepe ya bayyana.

“Jam’iyyar AK ce mafi girma haka kuma ita ce jam’iyyar da akasarin Turkawa suke ciki. Jam’iyyar AK ita ce jam’iyya daya da ake da ita a duka larduna 81 na Turkiyya, ba tare da la’akari da bambancin birni da kauye ba,” kamar yadda ya kara haske.

“Wannan ce jam’iyya daya da ke samun kuri’u daga duka kabilun Turkiyya da suka hada da Turkawa da Kurdawa da Larabawa da kabilar Laz da Circassia da ‘yan Bosnia da Georgia da kuma ‘yan Abkhazia kamar kowane lokaci.

Kuri’ar Kurdawa na da muhimmanci ga zaben Turikiyya, inda duka bangarorin ke neman goyon baya mai karfi.

Ga Jam’iyyar AK, bincike ya nuna foyon baya tsakanin Kurdawa ya karu matuka tsawon shekaru, kuma ana sa ran hakan zai nuna a zaben da za a gudanar a wata mai zuwa.

Adawa mai rauni

Irin raunin da bangaren adawa suke da shi wani dalili ne da ya sa suka kasa shawo kan masu zabe, kamar yadda jami’an Jam’iyyar AK suka bayyana.

Jam’iyyun wadanda ba su hada kansu ba sun mika Kilicdaroglu, wanda shi ne jagoran babbar jam’iyyar adawa ta CHP a matsayin dan takararsu, inda zai kara da Shugaba Erdogan.

Sauran abokan takarar sun hada da Muharrem Ince, tsohon dan Jam’iyyar CHP wanda Erdogan ya kada a zaben 2018 da kuma Sinan Ogan wanda shi kuma dan takarar ne da wasu jam’iyyu hudu da suka yi hadaka suka fitar a matsayin dan takararsu.

Dole ne dan takara ya samu da kashi 50 cikin 100 na kuri’u domin ya zama zababbe a zagayen farko. Idan cikin hudun babu wanda ya ci wannan adadin, jam’iyyun da suka ci adadi mafi yawa za su je zagaye na biyu wanda za a yi 28 ga watan Mayu.

TRT World