Sanarwar ta kara da cewa an kaddamar da bincike kan abin da ya haddasa fashewar. Hoto/AA

Akalla ma'aikata biyar sun mutu sakamakon fashewar wani abu a ma'aikatar kera makaman roka da sauran abubuwan fashewa da ke Ankara, babban birnin Turkiyya, a cewar Ma'aikatar Tsaron kasar.

"Wani abu ya fashe a ma'aikatar MKE Rocket and Explosives da ke lardin Elmadag a birnin Ankara. Sakamakon hakan, ma'aikatanmu biyar sun yi shahada," in ji sanarwar da ma'aikatar ta fitar ranar Asabar.

Ta kara da cewa an kaddamar da bincike kan abin da ya haddasa fashewar.

Ma'aikatar da abin ya fashe da sanyin safiya, mallakin kamfanin Machinery and Chemical Industry Corporation (MKE) na kasar Turkiyya ce.​​​​​​​

AA