Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya gana da takwarorinsa na Kazakhstan da Iraƙi da Lebanon da Gambiya da Tijikistan gabanin babban taron diflomasiyya na Antalya Diplomacy Forum wanda za a yi tsakanin ranar 1 zuwa 3 ga Maris.
Fidan da Ministan Harkokin Wajen Kazakhtan Murat Nurtleu sun tattauna kan dangantakar da ke tsakaninsu da kuma matakan da za su ɗauka na kyautata alakarsu a fannin tsaro ranar Ahamis.
Wasu majiyoyin diflomasiyya sun rawaito cewa ministocin biyu sun kuma tattauna kan yadda za su bunƙasa dangantakarsu a fannin ilimi da al'adu.
A lokacin ganawar tasu, sun ce ƙawancen da suka ƙulla kan kasuwanci inda suka yi hasashen zai kai na dala biliyan 10, yanzu ya zarta.
Ministocin biyu sun yi tattaunawa kan ayyukan da suke gudanarwa game da ci-gaban cinikayya da makamashi da sufuri.
Kazalika, Fidan da Nurtleu sun yi tsokaci kan harkokin ci-gaban yankinsu da kuma buƙatar haɗin-kai don ƙarfafa Majalisar Ƙasashen yankin Turkiyya wato Turkic Council.
Tattaunawa kan shirin Shugaba Erdogan na ziyartar Iraƙi
Lokacin da yake ganawa da takwaransa na Iraƙi Fuad Hussein, sun tattauna kan shirin shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan na kai ziyara ƙasarsu.
Bayan wani taro da aka yi tsakanin Turkiyya da Iraƙi a Ankara a watan Disamba, Fidan da Hussein sun tattauna kan shirin wannan taro da ake sa ran gudanarwa a birnin Bagadaza nan ba da jimawa ba.
Taron zai mayar da hankali kan yanayin tsaron Iraƙi da ci-gaban yankin da kuma wani shirin gina hanyoyi mai taken Development Road Project.
Samar da ci-gaba a Gaza
Fidan ya gana da takwaransa ministan Harkokin Wajen Lebanon Abdallah Bouhabib don tattauna kan abubuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma batun kawo ci gaba a Gaza.
Yayin tattaunawar, ministocin harkokin wajen biyu sun yi magana kan batun tsaro da zaman lafiya a Gaza da sauran yankin.
Ganawa da ministocin harkokin wajen Gambiya fa na TajikistanKazalika Fidan ya gana da ministan Harkokin Wajen Gambiya Mamadou Tangara da na Tajikistan Sirojiddin Muhriddin.
Babban jami’in harkokin diflomasiyyar Turkiyya ya bayyana jin dadinsa dangane da nasarorin da aka samu ta fuskoki da dama da Gambiya wacce daya daga cikin manyan kawayen Turkiyya ne a Afirka.
Kasashen biyu sun amince su karfafa huldarsu ta fuskar tsaro da tattalin arziki da al’adu.
Yayin ganawarsa da Muhriddin, an shirya manyan ziyarce-ziyarce a gaba daya shekarar kuma an dauki manyan matakai don karfafa hulda a fannin tsaro da ilimi da tattalin arziki.
Dangane da batun bayanan fa Muhriddin ya samar kan shata iyaka tsakanin Tajikistan da Kyrgyzstan, Fidan ya bayyana gamsuwar Turkiyya kan nasarar da aka samu ta wannan fuskar kuma yarjejeniyar da aka samu kuma ya ce yarjejeniyar da aka samu za ta taimaka wajen samar zaman lafiya da ci gaba a yankin.
Wakilai daga ƙasashe 147
Taron Diflomasiyya na Antalya zai karɓi baƙuncin wakilai daga ƙasashe 147.
Mutum kusan 4,500 ake sa rai za su halarci taron, ciki har da shugabannin ƙasashe 19 da ministoci 73 da wakilan ƙungiyoyin ƙasashen duniya 57.
Taron zai mayar da hankali kan batutuwa da suka haɗa da sauyin yanayi da ƙaura da yaƙi da ƙyamar Musulunci da ƙirƙirarriyar basira.
Mutum kusan 2,000 ne suka halarci taron a shekarar 2021. Kazalika, a 2022, an yi ƙananan taruka 30 daga cikin babban taron, yayn da a bana ake sa rai za a yi ƙananan taruka 52.