Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya soki Majalisar Ɗinkin Duniya kan gazawarta wajen nuna ingantaccen jagoranci da zai shawo kan ƙalubalen da duniya ke fuskanta a yau.
"Ƙasashen duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya na fuskantar jarrabawa a tarihi," Fidan ya faɗa wa Babban Taron MDD kan Makoma a birnin New York a ranar Litinin.
"Abin takaici, Majalisar Ɗinkin Duniya ta gaza nuna jogarancin da ya kamace ta na shawo kan barazanar da ke fuskantar ɗan'adam a yau."
Babban taron ya tattara shugabanni waje guda da manufar neman amincewar ƙasashe kan yadda za a samu makoma mai kyau.
Fidan ya ƙara da cewa ana buƙatar sabon tsari mai tasiri, wanda zai samar da mafita ta bai-ɗaya ga matsalolin duniya.
"Ana buƙatar gyaran da zai taɓo ko'ina"
"Muna buƙatar tsarin da zai taɓo kowanne ɓangare a ayyukan Majalisar Ɗinkin Duniya, musamman a Kwamitin Tsaro," in ji shi.
Tun da jimawa Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ke ta ƙoƙarin ganin an kawo sauyi a ayyukan Majalisar Ɗinkin Duniya inda yake amfani da taken "Duniya ta fi ƙasashe biyar girma," inda yake nufi da yadda babu adalci wajen zama mamba a Kwamitin Tsaro na Majalisar.
Erdogan ya kuma nuna rashin jin daɗi kan rashin tasirin da MDD ke da shi wajen magance rikice-rikive da dama a duniya, musamman yaƙin Isra'ila a Gaza da ya kusa shekara guda, wanda aka kashe mutane 41,000, mafi yawan su mata da yara, tare da jikkata fiye da mutum 95,000.