Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya caccaki Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙasashen yamma kan “zura ido suna kallon zalunci kan bil’adama” da Isra’ila ke aikatawa a Gaza tsawon kwanaki 140.
“Har ta kai ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ba zai iya kira kan a tsagaita wuta cikin gaggawa ba,” kamar yadda Erdogan ya koka a ranar Asabar, a lokacin da yake jawabi a wani taro na Jam’iyyar AK Party a lardin Sakarya da ke arewa maso yammacin Turkiyya.
“Kasashen Yamma ko Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya duk sun kasa taɓuka wani abu domin dakatar da Isra’ila daga rikicin da take yi,” kamar yadda ya jaddada.
Isra’ila na ta kai hare-hare a Gaza tun bayan da Hamas wadda Tel Aviv ta ce ta kashe mata mutum 1,200 a wani hari da Hamas ɗin ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
Yaƙin da Isra’ila ke yi a kan Gaza ya sa kaso 85 cikin 100 na jama’ar birnin sun rasa muhallansu a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarancin abinci da ruwan sha da magunguna inda aka lalata kusan kaso 60 cikin 100 na birnin, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar.
A karon farko tun bayan samar da ƙasar a 1948, ana zargin Isra’ilar da aikata kisan kiyashi a gaban Kotun Duniya, wadda ita ce kotu mafi girma ta Majalisar Ɗinkin Duniya.
Wani hukunci na wucin-gadi da kotun ta yanke ya bayar da umarnin ga Tel Aviv da ta dakatar da kisan kiyashin da take aikatawa da kuma ɗaukar matakai waɗanda za su tabbatar da an kai kayayyakin agaji a cikin Gaza.