Matar Shugaban Turkiyya Emine Erdogan na jawabi ga mahalarta shirin "A Starfish Story: Global Invitation to Volunteer Ambassadors" a hedkwatar UNICEF, a New York, Amurka ranar 25 ga watan Satumbar, 2024. / Hoto: AA

Matar Shugaban Turkiyya Emine Erdoga ta yi bayani kan shirin Jakadun Turkiyya na sa-kai (Gonul Elcileri Projesi) a wajen wata liyafar cin abinci da Matar Shugban Amurka Jill Biden ta shirya.

Da take magana a yayin taron, wanda aka gudanar yayin Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 79, Erdogan ta jadda cewa tabbatar da cewa kowane yaro ya samu gidan da zai rayu kuma a nuna masa ƙauna, hakkin ne a kan kowa. Ta jadda ƙudirin Turkiyya na tabbatar da walwalar yara a duniya.

A jawabin nata, uwargidan shugaban kasar ta bayar da shawarar fadada shirin ya wuce Turkiye, inda ta ce: "Na sami wannan mataki na yada shirinmu na Jakadun Sa-Kai, wanda ke da nufin tabbatar da tsaro dawalwalwar yaran da ke karkashin kariya, a matsayin mai matukar amfani."

Matar Shugaban na Turkiyya ta kaddamar da shirin na Jakadun Sa-kai ne a 2012, inda ya mayar da hankali kan samar da kulawa da tallafi irin na iyali ga yaran da aka tauye musu hakki. Shirin yana bunkasa daukar yara, yana nuna shi a matsayin wata hanya ta nuna wa yaran soyayya, da kuma kwantar musu da hankalin da suke bukata domin ci gabansu.

Erdogan ta jaddada cewa, kowane yaro ya cancanci ‘yancin tasowa a wajen da za su bunkasa, sannan shirin yana hada masu sa-kai da iyalai da ke daukar yara su hada kai da gwamnati don cim ma wannan aikin.

Ta hanyar hada kai da masu sa-kai da karfafa gwiwar iyalai da suke daukar yara, shirin yana da nufin rarraba ayyukan rainon wadannan yaran, don tabbatar da cewa sun samu tallafi wajen tunaninsu irin yadda suke bukata.

Manufar inganta rayuwar wadanda suke cikin hadari

Shirin da ke da ‘yan sa-kai fiye da miliyan biyu, ya sauya raywuar yara masu yawa a Turkiyya, musamman wadanda ake bai wa kulawa ta kariya.

Shirin ya zama wani ginshiki na manufofin kasar a bangaren zamantakewa, inda ake bunkasa tunanin cewa daukar yara domin kulawa da su ba wai kawai zabi ba ne, wata mafita ce ga yara da suka rasa iyalensu ko kuma aka raba su da su.

Erdogan ta kuma ba da shawarara fadada shirin a duka fadin duniya, tana nuna muhimmancin gaggauta shi, musamman a yankunan da tashe-tashen hankula suke addaba. Ta nuna cewa rikicin da ake yi a Gaza a matsayin wani babban misali, inda yara suke fuskantar yaki da yunwa da tsananin rashin kwanciyar hankali.

“Aikinmu gaba daya,” kamar yadda Erdogan ta bayyana, “shi ne mu bai wa yaran duniya da suka fitar da rai wadanda suke fafutuka da yakoki da hana musu damammaki, yanayin da za su ji suna da wani fata. Iyalai su ne mafari mai muhimmanci na sauya wannan bakar hanya.”

Shirin wanda tuni aka jinjina masa saboda hanayar da ya fito da ita wajen daukar yara, ya sauya tsarin kula da walwala na Turkiyya tun bayan kaddamar da shi a 2012.

Ta hanyar jakadun zuciya, Turkiyya tana so ta ja hankalin sauran kasashe su fito da irin tsarin na dabarun kula da walwalar yara, wanda yake tabbatar da cewa duka yara, ba tare da kula da inda suka samu kansu ba, sun samu damar tasowa a wajen da ake son su kuma ake karfafar su.

Irin yadda ta zama tauraruwar shiri na Zukatan Jakadu a matsayin abar misali, Emine Erdogan ta sa Turkiyya ta zama jagora wajen tunkarar daya daga manyan matsalolin da mutane ke fuskanta a zamaninmu: kare hakkoki da rayuwar goben yaran da suka fi fuskantar matsala.

TRT World