Matar shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan ta tuna da kisan kiyashin Srebrenica da aka yi shekaru 29 da suka wuce, inda ta kira lamarin da 'abun kunya' a tarihin bil'adama.
"Ina sake sukar kisan kiyashin Srebrenica, wanda ya bautar da yankunan Bosniyawa, ya sanya su baƙin ciki da hawaye. Wannan babi ne na abin kunya a tarihin ɗan'adam, a lokacin da aka cika shekara 29 da mummunan lamarin," ta bayyana a shafinta na X.
"Ina tuna wa da 'yan'uwanmu na Bosnia da aka dauke daga cikinmu kuma ina jin irin radadin da iyalansu ke ji," in ji Emine Erdogan
A hukumance Turkiyya ta ayyana ranar 11 ga Yuli a matsayin "Ranar Kasa da Kasa ta Tunawa da Kisan Kiyashin Srebrenica", kamar yadda wata dokar da Shugaban Ƙasa ya sanya wa hannu da aka buga a jaridar gwamnati a ranar Laraba ta faɗa.
Kisan kiyashin Srebrenica
A lokacin bazarar 1993 ne, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya ayyana Srebrenica a matsayin "yanki mai amana". Sai dai kuma sojojin Serbia karkashin Janaral Ratko Mladic, wanda daga baya aka samu da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil'adama da aikata kisan kiyashi, ya afka wa yankin da ke karkashin kariyar MDD.
Dakarun Netherland da ke da hakkin kare jama'a a yankin na MDD, sun gaza yin wani abu a lokacin da sojojin Serbia suka mamaye yankin a ranar 11 ga Yili, tare da kashe mutum 2,000 a rana guda da suka hada da yara ƙanana.
Kusan Bosniyawa 15,000 ne suka gudu zuwa tsaunukan yankin, amma sojojin Serbia suka bi su, suka saske kashe mutum 6,000.
Sojojin Serbia sun bai wa mata da yara kanana izinin zuwa yankunan da ke karkashin ikon Bosnia, amma sun kashe maza Bosniyawa 8,372 a dazuka, masana'antu da wuraren ajiye kaya.
An binne Bosniyawan da aka kashe a manyan kaburbura, inda aka gano gawarwaki a wurare 570 daban-daban da ke cikin kasar, ciki har ba ramuka 77 da aka binne mutane da dama a cikinsu.
A 2007, kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa da ke Hague ta yanke hukuncin cewa an aikat Kisan kiyashi a Srebrenica.
An ci gaba da ayyukan neman wadanda ba a gani ba a yankin, inda a kowacce shekara ake binne kasusuwan mutanen da aka gano a Makabartar Tunawa da su.
Ya zuwa yau, an binne mutane 6,751 a wannan makabarta, an kuma binne wasu 250 a sauran makabartun garuruwa sakamakon bukatar hakan da 'yan'uwansu suka nuna. Har yanzu ana ci gaba da neman sama da mutane dubu daya.
A ranar 8 ga Yunin 2021, alkalan kotun MDD sun amince da hukuncin daurin ra da rai ga Mladic saboda aikata kisan kiyashi, zaluntar mutane da cin zarafin ɗan'adam da karar da jama'a da wasu manyan laifuka da aka aikata a Bosnia da Herzegovina.
A yayin tuna wa da ranar ta wannan shekarar, za a binne kasusuwan mutane 14 da aka tabbatar an kashe a lokacin kisan kiyashin babbar makabartar tuna wa da su.