Nuh Yilmaz ya jaddada bukatar ƙara wa Isra'ila da kawayenta matsin lamba domin samar wa Falasdinu adalci, sannan ya yi ƙira ga sauran kasashen duniya kan su ci gaba da nuna goyon bayansu ga  Falasdinawa. / Hoto: AA  

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Nuh Yilmaz ya soki gwamnatin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu kan tashe-tashen hankula da suka mamaye yankin Gabas ta Tsakiya.

A yayin taron Ƙungiyar Haɗin kan Ƙasashen Musulmi ta OIC a birnin Jeddah a ranar Laraba, Yilmaz ya zargi gwamnatin Netanyahu da tsageranci da nuna wariyar launin fata, yana mai cewa da gangan ta jefa yankin cikin ruɗani don cim ma manufarta ta siyasa.

Ya yi nuni da kisan gillar da aka yi wa shugaban ofishin siyasa na Hamas Ismail Haniyeh a matsayin misali, yana mai bayyana mummunar aika-aikar da barazanar dakile koƙarin da ake yi na samar da zaman lafiya.

Yilmaz ya jajanta mutuwar Haniyeh, wanda aka kashe a Iran a ranar 31 ga watan Yuli, ya kuma yi tir da kisan a matsayin abin kunya da ya keta hurumin kasar Iran.

Ya kara da cewa matakan da Isra'ila take ɗauka suna barazana ga yankin tare da take dokokin kasa da kasa.

Yilmaz ya kuma jaddada goyon bayan Turkiyya ga Falasdinu, yana mai cewa har yanzu gwagwarmayar Falasdinawa tana nan daram, duk da hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da yi.

Kafa kasashe biyu masu cin gashin kansu

Da yake ƙarin haske kan mamayar da Isra'ila ke ci gaba da yi a yankunan Falasdinawa, Yilmaz ya ce mafita ɗaya ta samun zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ita ce idan har za a kawo ƙarshen mamayar Isra'ila da kuma samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu bisa ga yarjejeniyar iyakoki na shekarar 1967.

Ya soki yadda Isra'ila ta yi watsi da kiran ƙasashen duniya kan a tsagaita wuta a Gaza da kuma hana kai ayyukan jinƙai yankin, inda ya ce a baya-bayan nan ne majalisar dokokin Isra'ila ta zartar da dokokin da suka ƙi amincewa da kafa kasar Falasdinu tare da ayyana hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasdinu (UNRWA) a matsayin kungiyar ta'addanci.

Yimaz ya yi gargadin cewa idan ba a dakatar da Isra'ila ba, Netanyahu na iya fadada rikicin, wanda zai haifar da mummunan sakamako ga yankin da ma sauran kasashen duniya.

Ya kuma soki kasashen duniya musamman ma Majalisar Dinkin Duniya da gazawa wajen hana zubar da jini, ya kuma soki 'yan majalisar dokokin Amurka da suka jinjinawa Netanyahu a ziyarar da ya kai birnin Washington a baya-bayan nan, yana mai cewa ko suna murna da kisan ƙare dangi da yake yi ne.

TRT World
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince