Matar Shugaban Kasar Turkiyya Emine ta karbi kambin Majalisar Dokokin Yankin Bahar Rum (AKDENIZ-PA) saboda shirinta na ‘Zero Waste’. / Hoto : AA

Matar Shugaban Kasar Turkiyya Emine ta karbi kambin Majalisar Dokokin Yankin Bahar Rum (AKDENIZ-PA) saboda shirinta na ‘Zero Waste’ da take bayar da gudunmawar da take bayarwa ta zaman lafiya da bunkasa a yankunan Turai Bahaar Rum da Gulf.

Ministan Muhalli Mehmet Ozhaseki ne ya karbi kambin a madadin Shugaba Recep Tayyip Erdogan da mai dakinsa Emine Erdogan a wajen bikin da aka gudanar a Braga, Portugal a ranar 15 ga Mayu.

“Na yi farin cikin karbar kambin AKDENIZ-PA a madadin dukkan abokan sararin duniyar nan da suka rungumi wannan shiri, suka ciyar da shi gaba da gudunmawarsu, sannan suka kai shi ga al’lummu na gaba” in ji mai dakin shugaban kasar.

Emine Erdogan ta jaddada cewa Turkiyya na matukar alfahari kan yadda aka zabi shirin Zero Waste a matsayin shirin da ya fi kowanne bayar da gudunmowa wajen kare muhalli a tsakanin wasu shirye-shiryen da yawa, kuma aka ba shi kambin kasa da kasa.

“Ina kallon wannan kambi ba wai a matsayin takardar nasara ba, sai a matsayin alamarmayar da hankalin da Turkiyya ta yi wajen wayar da kan jama,a game da muhallidamatakan da take dauka na samar da makoma mai inganci.” in ji ta.

Kambin da shirin ‘Zero Waste’ ya lashe

A 2017 aka kaddamar da shirin Zero Waste karkashin jagorancin mai dakin shugaban Turkiyya Emine Erdogan, kuma ya zuwa yanzu shirin ya lashe kambi da dama.

A 2018, shirin ya karbi kambin “Zero Waste, Zero Hunger” (Babu Tara Bola, Babu Yunwa) daga Hukumar Bunkasa Ayyukan Noma da Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO).

A shekarar 2021, shirin la lashe “Kambin Manufofin Cigaba Mai Dorewa na UNDP” da ke karkashin Shirin Cigaba na Majalisar Dinkin Duniya, da “Kambin Waste Waste Cities Champion Global Award” da ke karkashin Shirin Samar da Matsugunai ga Mutane na MDD.

A 2022, shirin ya lashe “Kambin Majalisar Kasashen Yankin Bahar Rum (PAW Awards)” da “Shugabancin Kare Yanayi da Cigaba” wanda Bankin Duniya ke Bayarwa.

Shirin “Turkiye Zero Waste” wanda ya zama babbar haja a duniya saboda kokarinsa na tabbatar da tsaftatacciyar Turkiyya, kasa mai cigaba da dorewa ta hanyar rage yawan bola da ake tara w, sai a dinga sarrafa ta zuwa wasu kayayyaki, ya samu shiga jerin shirye-shiryen neman lashe kambin Babban Taron MDD da aka yi a Dubai a 2022.

TRT World