Likitocin Turkiyya a Amurka sun kirkiro wani rigakafi da zai taimaka wajen hana yaduwar cutar kansar mama a jikin dan adam.
An fara gwajin rigakafin ne a asibiti kan wasu mutum 10 da suka ba da kansu, daga nan kuma ana sa ran fadada shi zuwa kan wasu karin mutum 50, a cewar Atilla Soran, kwararre a fannin tiyatar mama da ke jagorantar aikin binciken.
Binciken da suka yi a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jami'ar Pittsburgh ya ja hankalin jama'a sosai a Amurka, kuma kafofin watsa labarai sun bayyana shi a matsayin wani "muhimman ci gaba".
Cutar kansar mama tana daga cikin nau'in cututtuka na kansa da aka fi sani a tsakanin mata, ba wai a kasar Amurka kawai ba amma a duk fadin duniya, ciki har da kasar Turkiyya, a cewar Soran.
"Muna tunanin wannan maganin rigakafi zai hana yaduwar cutar kansar mama a jikin dan'adam." a cewar Farfesan na Turkiyya.
"Abu mafi mahimmanci da kungiyar binciken, ciki har da ni, ta cimma shi ne cewa rigakafin da aka samar kuma aka gwada ingancinsa a dakin gwaje-gwaje har na tsawon wasu shekaru ya samu fita zuwa asibitoci don gwajinsa."
Za a sa ido kan wadanda suka ba da kansu wajen gwada wannan rigakafi na tsawon shekaru biyar masu zuwa, bayan nan ne za a iya amincewa da amfani da shi a manyan wuraren gwaje-gwaje na asibitoci da kasuwanni.
Nau'in cutar daji na biyu mafi muni
Cutar kansar ta mama, ta kasance ta biyu mafi muni bayan cutar huhu a tsakanin mata, in ji Soran.
Kimanin mata 360,000 ake sa ran za a musu gwajin cutar kansar mama a Amurka a shekarar 2023, in ji shi, ya kara da cewa kashi 16 cikin 100 ne kawai daga cikin adadin mutanen za a iya kai ga tantance cutar da wuri a jikinsu.
"Idan allurar rigakafin ta fara aiki a daidai wannan lokaci, to muna tunanin za mu iya hana yaduwar cutar a jikin mai dauke da ita akalla wani bangare mai girma na wadannan mata 360,000," in ji shi.
Soran ya kara da cewa gwaje-gwajen asibiti da ake yi kan rigakafin ba ya tafiya cikin sauri saboda cutar kansar ta mama ba ta haifar da wani babban hadari kamar cutar Covid-19.
Bayan an gayyace shi zuwa Amurka a shekarar 1997 don yin aiki a matsayin kwararre, Soran ya zama mutum na farko da ya sami matsayin farfesa a 2004 a Sashen Mammaplasty na Jami'ar Pittsburgh.
A shekarar 2007, ya bayyana bincikensa da ya yi karin haske kan ci-gaban da aka samu a cutar "Binciken Turkiyya". Har yanzu ana amfani da irin sa a fadin duniya.