Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira kan a kare hakki da tabbatar da jin dadin al'ummar Turkawa a Turai.
"A lokacin da ake samun barazana daban-daban, tun daga kin jinin Musulunci zuwa ga nuna wariyar al'ada na kara karuwa a Turai, babban aikinmu a matsayinmu na kungiya shi ne kare 'yanci da muradin Turkawa da ke Turai ba tare da kauce wa tsarin dimokuradiyya da doka ba," kamar yadda Erdogan ya bayyana a ranar Asabar a wani sako ta bidiyo da ya aika wa kungiyar kasa da kasa kan dimokuradiyya, da ke a Cologne, a kasar Jamus.
Erdogan ya ce domin cimma wannan burin akwai bukatar a yi wannan gwagwarmayar da kishi, bisa tsarin doka da oda, tare da hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kansu na Turkiyya da kuma amfani da kafafen watsa labarai.
Muna sa ran za ku ƙara ba da gudunmawa ga siyasa, zamantakewa, tattalin arziki, al'adu, da kimiyya a kasar da kuke zama," kamar yadda ya kara da cewa.
Erdogan ya yi kira da a koya wa yara al'adunsu, da kuma dabi'u na wayewa. "A kowane lokaci a tuna da wannan: Babban makaminmu na yaki da sauya al'adunmu shi ne koya wa ƴaƴanmu harshensu na uwa da al'adarsu da kuma ilimin zamani, da kuma tabbatar da tabbacin makomarmu," kamar yadda shugaban na Turkiyya ya bayyana.
Shugaba Erdogan ya bayyana cewa yana da yakinin kungiyar ta kasa da kasa kan dimokuradiyya za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace ta wannan fannin ba tare da shakka ba.
"Da fatan a cikin wannan gwagwarmaya mai ma'ana mai muhimmanci, kamar yadda muka kasance tare da ku tsawon shekaru 20 da suka gabata, za mu ci gaba da kasancewa tare da ku.
"Ina rokon Allah ya taimake mu. Ina mika soyayyata da gaisuwa ga duka 'yan kasarmu da ke zaune a wajen Turkiyya, musamman a Turai ta hanyarku. Ina fatan majalisar ku za ta sake zama mai albarka," in ji shi.