Turkiyya ta zabi Gezeravci, wani Sojan Saman kasar da ke tura jirgin F-16, a matsayin dan kasar na farko da zai tafi sararin samaniyar a shekarar da ta gabata yayin taro kan fasaha na TEKNOFEST. / Hoto: AA Archive

Jirgin sama-jannatin Turkiyya na farko zai tafi Tashar Sararin Samaniya [ISS] da misalin karfe daya da minti goma na dare agogon kasar a ranar 18 ga watan Janairu, a cewar wani babban jami'in kasar da kuma hukumar sararin samaniya ta Amurka NASA.

Kanar Alper Gezeravci da tawagarsa za su shiga jirgin sama-jannatin mai suna Axiom Mission 3 [Ax-3] zuwa tashar ta sararin samaniya ta ISS, in ji Ministan Masana'antu da Fasaha na Turkiyya Mehmet Fatih Kacir a sakon da ya wallafa a shafin X ranar Alhamis.

"Wannan tafiya mai dimbin tarihi za ta za karfafa gwiwar al'umma mai zuwa da kuma kasancewa wani muhimmin mataki a kimiyyar sararin samaniya ta Turkiyya," a cewar Kacir.

Rokar Falcon 9 ta kamfanin SpaceX ce za ta harba tawagar ta Ax-3 a cikin kumbon Dragon cibiyar Kennedy da ke birnin Florida na Amurka zuwa sararin samaniya

Ana sa rai kumbon zai sauka a Tashar Sararin Samaniya ranar 19 ga watan Janairu da misalin karfe daya da kwata na rana.

Hatimi na musamman

Hukumar da ke bincke kan fannin Sararin Samaniya ta Turkiyya [TUA] da hukumar aikewa da wasiku ta kasar PTT, sun zayyana wani hatimi na musamman da za a sanya a cikin jirgin sama-jannatin, sannan Gezeravci zai daga tutar Turkiyya a sararin samaniya.

Hatimin na dauke da wasu alamomi, da ke nuna manufar balaguron na 'yan kasar ta Turkiyya, da kuma wani zane na musamman na Gezeravci yana rataye da tutar kasar a kafadarsa.

TRT World