Jirgin ruwa dauke da tan 2,955 na kayan agaji, da aka tattara karkashin Hukumar Agajin Gaggawa ta Turkiyya (AFAD), ya bar tashar jiragen ruwa ta Mersin zuwa Sudan.
Tare da hadin giwar AFAD da Ofishin Gwamnan Mersin, da taimakon ma'aikatar HArkokin Waje, Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Crescent ta Turkiyya da wasu kungiyoyin da ba na gwamnati ba su 12, an tattara kayan zuwa Sudan.
Kayan tallafin mai yawan tan 2,955, sun hada da kayan abinci, tsafta, wuraren kwana d ana kula da lafiya, tare da injinan bayar da lantarki, tantuna, da dakin gasa biredi na tafi da gidanka, an loda su a jirgin ruwa mai suna "Sea Horse".
Da yake jawabi a wajen taron tura jirgin a tashar jiragen ruwa a ranar Litinin, mataimakin shugaban AFAD Hamza Tasdelen ya ce za su tura jirgin ruwa na biyu da kayan tallafi zuwa Sudan.
Ya kara da cewa "yau mun taru a nan don aika kusan tan 3,000 na kayan taimako. Kayayyakin sun hada da tantuna 18,500, sama da barguna 17,000 da kayan amfani da dama, tan 10,000 na garin fulawa da kusan tan 500 na sauran kayan abinci."
Tasdelen ya ambaci cewa a ranar 19 ga Yuli ne jirgin ruwan farko da suka aika ya isa Sudan dauke da tan 2,500 na kayan agaji.
Ya yi tsokaci da cewa akwai matsaloli a yankin kusa da Turkiyya, ciki har da yakin basasar da ake ci gaba da yi, fari da yawaitar ruwan sama.
Da yake karin haske kan irin taimakon da ake baiwa Sudan, Tasdelen ya ce "Kasarmu na ci gaba da tallafa wa dukkan bani adam, ba tare da kallon yanki, yare ko launin fata a fadin duniya."
Karin jiragen ruwa hudu zuwa Gaza
"Muna mika tsantsar godiyarmu ga kungiyoyin da ba na gwamnati ba da muke da su da Kungiyar Red Crescent. Kamar koyaushe, mun shirya kayan taimakon tare da su gaba daya."
Ba wannan ne karo na farko da muka yi hakan ba. Wannan ne karo na 14 da muka aika kaya a wannan shekarar. Mun tura 12 zuwa Masar don kai wa Gaza.
Mun kuma samar da muhimman kayan agaji a can. A yanzu haka, mun tura tan 75,000 zuwa Gaza," in ji shi.
Tasdelen ya jaddada cewa a karkashin jagorancin Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da umarnin Ministan Harkokin Cikin Gida Ali Yerlikaya, an dauki matakin aika tan 30,000 na garin fulawa zuwa Gaza.
Ya kara da cewa za su kai wannan garin fulawar zuwa Gaza a jiragen ruwa tara. "Ya zuwa 13 ga Satumba, mun kammala aika jirgi na biyar.
Kuma a duk kwanaki 10 za a tura jirage hudu, inda za a kai jimillar tan 30,000 na garin fulawa zuwa Gaza."
Tasdelen ya kuma ambaci wahalar da ake sha kafin wuce kofar Rafah, yana mai cewa "Muna da kaya da ke jiran a bar su su shiga Gaza.
Da zarar mun kawar da matsalolin nan na shiga Gaza, za mu kai motocin da suke jira dauke da kayan talafin zuwa Gaza ta kofar iyaka ta Rafah."