Jam'iyyar AK mai mulki a Turkiyya na ci gaba da sanar da sunayen 'yan takararta a zabe mai zuwa

Jam'iyyar AK mai mulki a Turkiyya na ci gaba da sanar da sunayen 'yan takararta a zabe mai zuwa

Turgut Altinok ne zai tsaya takara a Ankara, yayin da Hamza Dag kuma zai tsaya a Izmir a zaben 31 ga Maris karkashin tutar jam'iyyar AKP.
A ranar 31 ga Maris, masu zabe za su jefa kuri'a don zaben magajin gari da na gundumomi da masu unguwanni a fadin kasar. Hoto: AA

Shugaban kasar Turkiyya kuma jagoran jam'iyyar AKP ya sanar d akarin sunayen 'yan takarar magajin garin 48 da za a fafata da su a zaben watan Maris.

A ranar Alhamis din nan, shugaba Erdogan ya sanar da Turgut Altinok da Hamza Dag a matsayin 'yan takarar AKP na magajin garin Ankara da Izmir.

Bayan taron jam'iyyar a babban birnin Ankara a farkon watan Janairu ne shugaba Erdogan ya sanar da sunayen sauran 'yan takararsu na manyan larduna 17 da kananan larduma 31.

Da ma tuni Erdogan ya sanar da sunan Murat Kurum, wanda a yanzu dan majalisar dokokin Turkiyya ne da a baya ya rike mukamin Ministan muhalli da raya birane, a matsayin dan takarar magajin garin Isranbul na jam'iyyar.

Hukumar Zabe ta Koli ta Turkiyya ta sanar da cewa jam\yyu 36 ne suka cancanci shiga zaben na 31 ga Maris.

Hukumar ta ce a ranar 17 ga janairu za a kammala fitar da rajistar masu jefa kuri'a, sannan a ranar 27 ga Janairu kammala saka alamar kowacce jam'iyya a jikin takardar zabe.

Nan da 31 ga Janairu ne ya zama lallai kowacce jam'iyya ta kammala mika sunayen 'yan takararta. Za a fara fitar da takardun zaben daga 16 ga Fabrairu.

A ranar uku ga Maris za a fitar da sunayen 'yan takara na karshe, za kuma a gama yawon gangamin zabe daga ranar 21 zuwa 31 ga Maris.

A ranar 31 ga Maris, masu jefa kuri'a za su zabi magajin garin larduna da na gundumomi, tare da masu unguwanni a fadin kasar.

TRT World