Jami'an leƙen asirin Turkiyya da haɗin gwiwar 'yan sandan ƙasar sun kama Aslan a ranar Asabar a birnin Istanbul, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar.
Jami'an leƙen asirin na Turkiyya sun jima sun bibiyar yar ta'addar, wadda ta taka muhimmiyar rawa a wasu daga cikin ayyukan da ƙungiyoyin PKK da KCK ke yi a Australia.
An gano cewa Aslan, wadda ke da alaƙa da ƙut da ƙut da manyan 'yan ta'dddan ƙungiyoyin, na kan hanyarta ta zuwa Australia daga filin jirgin Istanbul.
Bayan an kama ta, alƙali ya aika da ita gidan yari.
A tsawon shekara 40 da kungiyar ta yi tana ta'addanci a Turkiyya - kasar Turkiyya da Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai sun ayyana PKK a matsayin kungiyar ta'addanci wacce ke da alhakin mutuwar mutum kusan 40,000 da suka hada da mata da yara har da jarirai.