Jami'an leken asirin Turkiyya sun 'kawar da' 'yan ta'addan PKK da dama a 'yan kwanakin nan. Hoto/AA

Jami’an leken asirin Turkiyya sun ‘kawar da’ wani babban dan ta’adda na kungiyar PKK/YPG a wani samame da suka kai arewacin Syria, kamar yadda majiyoyin tsaro suka tabbatar.

Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) ta ‘kawar da’ Haydar Demirel a ranar Asabar, wanda ake wa inkiya da Bager Turk wanda kuma shi ne ake ikirarin shugaban kungiyar ta’addancin a lardin Hol da ke arewacin Syria, kamar yadda majiyoyin tsaro wadanda suka bukaci a sakaya sunansu suka bayyana saboda takunkumin da aka saka musu na yi wa ‘yan jarida magana.

Hukumar ta MIT wadda ke neman dan ta’addan tun a 2020, ta rutsa shi ne a yayin da yake horas da mayakan PKK/YPG a arewacin birnin Tal Hamis da ke Syria.

Kamar yadda hukumomi suka bayyana, Demirel ya shiga kungiyar ne tun a 1993 kuma ya samu horo daga shugaban kungiyar wanda aka kama Abdullah Ocalan tsakanin 1993 da 1994 a Syria, inda kuma yake da hannu a ayyukan ta’addanci da dama a Syria.

Ko a kwanakin baya sai da Jami’an leken asirin Turkiyya suka “kawar da” wani babban dan ta’adda na kungiyar YPG/PKK a arewacin Syria Mehmet Sari, wanda aka fi sani da Baran Kurtay.

Haka kuma jami’an sun ‘kawar da’ Eyvaz Beyaz, wani dan kungiyar ta’addanci ta PKK da ake nema ruwa-a-jallo, a wani samame da da kai a arewacin Iraki.

Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana PKK a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda – kuma ta jawo mutuwar sama da mutum 40,000 ciki har da mata da kananan yara.

Hukumomin Turkiyya suna amfani da “kawarwa” domin nuna cewa dan ta’addan ko dai ya mika kansa ko an kashe shi ko an kama shi.

TRT World