Hukumar leken asiri ta Turkiyya ta 'kassara' jagoran 'yan ta'addar PKK/YPG a garin Aynul Arab na arewacin Siriya, in ji majiyoyin tsaro.
A farmakin da aka kai a wajen iyakar Turkiyya, Hukumar Leken Asiri (MIT) ta 'kassara' Mutlu Kazar, da ake wa lakabi da Karker Andok, wanda shi ne babban jagoran kungiyar ta ta'addncia a gundumar Aynul Arab, in ji majiyar a ranar Litinin.
Jami'an tsaron Turkiyya na amfani da kalmar 'kassarawa' da nufin an kashe ko kama dan ta'adda, ko kuma ya miƙa wuya.
Kacar da ya shiga kungiyar ta'addancin a 1997, kuma yake da hannu a hare-haren ta'addanci da dama a yankin haftanin na arewacin Iraki a 2009, ya samu raunuka a hannu a idonsa yayin arangama da jami'an tsaro.
Kasancewar ayyana shugabancin Sansanin Makhmur Rustem Cudi da ke arewacin Iraki a 2013, yankin Tel Rifat na Siriya a 2015 da kuma shugabancin mayakan PKK/YPG a Tel Rifat a 2020, ya sanya Kacar a farkon wannan shekarar ya zama babban jagoran ƙungiyar a Aynul Arab.
A 2022, ya je Al-Malikiyah da ke arewacin Siriya. Shekara guda kafin hakan, ya bayar da umarnin kai hari kan jerin gwanon motocin jami'an tsaron Turkiyya da ke kai Farmakan Firat a arewacin Siriya, wanda hakan ya yi ajalin sojoji a ranar 24 ga Yuli, 2021.
Tun shekarar 2016, Ankara ta ƙaddamar da farmakan yaƙi da ta'addanci cikin nasara a iyakokinta da arewacin Siriya, da manufar hana kafa matattarar 'yan ta'adda a yankin, da kuma bayar da damar samar yankunan zaman lafiya ga jama'a.
Bayan MIT ta gano maboyar ɗan ta'addan mai suna Mutlu Kacar da ake wa laƙabi da Karker Andok a arewacin Siriya ne aka kai farmaki tare da kassara shi.
A hare-hare ta'addanci da take kai wa Turkiyya a cikin shekaru 35, ƙungiyar PKK ta shiga jerin sunayen ƙungiyoyin ta'adda a Turkiyya da Amurka da Tarayyar Turai -- wadda ke da alhakin mutuwar sama da mutum 40,000, da suka hada da mata da yara ƙanana da jarirai.
Ƙungiyar YPG ita ce reshen PKK a Siriya.