Hukumar Leken Asirin Turkiyya ta dakile shirin Kungiyar Daesh na kai hari arewacin Syria

Hukumar Leken Asirin Turkiyya ta dakile shirin Kungiyar Daesh na kai hari arewacin Syria

An kama wasu 'yan ta'addar kungiyar Daesh uku dauke da bama-bamai da da harsasai da ke shirin kai hari arewacin Syria.
Jami'an Turkiyya sun ba da rahoton cewa mutane ukun da aka kama manya ne a kungiyar Daesh. . Hoto: OTHERS

An kama wasu 'yan ta'addar kungiyar Daesh ta hanyar hadin gwiwa tsakanin Hukumar Leken Asirin Turkiyya (MIT) da kuma Rundunar Sojin Syria (SNA).

Jami'an tsaro na rundunar SNA sun gudanar da samame a arewacin Syria karkashin taimakon hukumar leken asiri ta MIT, a yankin da rundunar tsaron Turkiyya ke aiki.

Jami'an Turkiyya sun ba da rahoton cewa mutane ukun da aka kama manya ne a kungiyar Daesh.

Abubuwan da aka kwace a hannunsu sun hada da makami daya na kakkabo tankokin yaki (M72LAW), makami daya na RPG da sauran manyan makamai da jigidodin harsasai.

AAn kama makamai da dama a hannun 'yan ta'addan. Hoto: OTHERS

A yayin da Turkiyya ke ci gaba da kokarinta na yaki da kungiyoyin ta'addanci da suka hada da Daesh da Al-Qaeda da kuma PKK ba tare da nuna wani bambanci ba, hukumar leken asiri ta MIT ta Turkiyya na ci gaba da zage damtse wajen yaki da kungiyoyin 'yan ta'addar a Syria da sauran yankin, da nufin kare kasar daga barazanar tsaro.

A shekarar 2013, Turkiyya ta zama cikin kasashe na farko da suka ayyana Daesh a matsayin kungiyar ta'addanci.

Kasar ta sha fama da da hare-hare daga kungiyar Daesh a lokuta da dama, inda aka kashe fiye da mutum 300 tare da jikkata daruruwan mutane a hare-haren kunar bakin wake a kalla 10, da harin bam bakwai da kuma harin 'yan ta'adda hudu da aka kai.

A martaninta, Turkiyya ta kaddamar da ayyukan yaki da ta'addanci a gida da waje don kare hare-haren da za a iya kai mata.

TRT World