Altun ya jaddada cewa labaran da Anadolu Agency ke wallafawa da suka haɗa da hotuna na musamman a harsuna 13 sun sa kamfanin ya zama wata babbar murya a harkokin watsa labarai na duniya. / Hoto: AA

Daraktan Sadarwa na Ofishin Shugaban Ƙasar Turkiyya Fahrettin Altun, ya taya kamfanin dillancin labarai na ƙasar Anadolu Agency murnar cika shekara 104 da kafuwa, yana mai cewa kamfanin yana taka muhimmiyar rawa a yaƙin da ƙasar take yi da masu watsa labaran ƙarya.

Altun ya jinjina wa kamfanin dillancin labaran wajen kasancewa wata kafa da aka dogara da ita wurin samun sahihan labarai, musamman a wannan zamani da ci-gaban hanyoyin sadarwa ya bijiro da buƙatar bayar da labarai na gaskiya.

Ya bayyana irin karɓuwar da Anadolu Agency ya yi a duniya, inda yake da wakilai a ƙasashe fiye da100 da ofisoshi a ƙasashe 41 countries, abin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin kafofin watsa labarai mafi girma a duniya.

Altun ya jaddada cewa labaran da Anadolu Agency ke wallafawa da suka haɗa da hotuna na musamman a harsuna 13 sun sa kamfanin ya zama wata babbar murya a harkokin watsa labarai na duniya. Ya bayyana yadda kamfanin yake fayyace gaskiya a cikin labaransa inda yake fito da irin gazawar kafofin watsa labaran yammacin duniya, musamman a yankuna irin su Gaza.

Da yake bayyana rawar da Anadolu yake takawa wurin fayyace batutuwan da suka shafi shari'a, Altun ya ce kamfanin ya yi amfani da alƙaluma da hotuna wajen fito da laifukan yaƙin da Isra'ila take aikatawa.

TRT World