Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da majalisar dokokin kasar shirinta na sayar wa Turkiyya na'urar Link-16 da za ta inganta aikin jiragen yakinta samfurin F-16.
A wata sanarwar da ta fitar ranar Litinin, hukumar tsaron Amurka ta ce ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ba da damar sayar wa Turkiyya kayayyaki da manhajoji na tsaro da za su inganta jiragen yakinta samfurin F-16 da kuma wasu kayayyakin aiki kan $259m.
"Hukumar tsaro ta Amurka ta ba da takardar shaidar da ake bukata kuma ta sanar da majlisar dokokin kasar kan yiwuwar sayarwa Turkiyya wadannan kayayyaki," in ji sanarwar.
Ababen da za a iya sayarwar sun hada da kayayyakin da suka jibanci tsaro da kuma ilimin taimakon fasaha na inganta na’urar Link-16 mai musayar bayanai da ke cikin jiragen yakin Turkiyya samfurin F-16 zuwa mataki na biyu (Wato Block Upgrade-2 level), tare da na’urar kauce wa karo a kasa.
Majalisar dokokin Amurka na da ‘yancin kin amincewa da bukatar ma’aikatar wajen Amurka nan da kwana 15.
Link-16 wata na’ura ce ta musayar bayanan soji wato tactical data link (TDL), wadda kasashen kungiyar Nato da kawayensu ke amfani da ita.
Tana ba da damar musayar bayanai da dabaru tsakanin jirage da jirage masu saukar ungulu da jirage marasa matuka da jiragen ruwa da kuma dakarun da ke doron kasa.
Ankara da Washington sun yi yarjejeniya a bara kan sayen sabbin jiragen yaki samfurin F-16 guda 40 da kuma kayayyakin sabunta jiragen guda 79.
Sai dai ana jiran amincewar majalisar dokokin Amurka kafin aiwatar da yarjejeniyar.