Turkiyya na sane da yadda kungiyoyi na ta’addanci ke "amfani da kalamai da diflomassiya da dabarun soji", in ji Erdogan . (AA)

Matakin da ya kebanta makomar bil’adama a hannun kasashe biyar ba abu bane mai dorewa ba, a cewar shugaban kasar Turkiyya, inda ya bukaci a samar da hadin kai tare da yi wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya garambawul.

A wani taron liyafar buda baki da aka gudanar a ranar Talata a Ankara tare da jakadun kasashen waje da jami'an diflomasiyya, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce "Tsarin da ake yi a halin yanzu, ya dabaibaye makomar bil'adama tsakanin kasashe biyar, wanda ba abu bane mai dorewa, akwai bukatar a yi wa Kwamitin Tsaro na MDD garambawul cikin gaggawa tare da fahimtar da juna da samar da hadin kai."

Ya ce, a halin da ake ciki ''Turkiyya na ci gaba da girban abin da ta shuka’’ na tsarinta na kasuwanci da aikin ba da agaji, inda kasashe da dama suka yi gaggawar kawo dauki ga Turkiyyar bayan iftila’in girgizar kasa da aka yi a ranar 6 ga watan Fabrairu a kudancin kasar.

Rikicin Ukraine

Dangane da yakin da Rasha ke yi da Ukraine, Erdogan ya yi imanin cewa akwai ‘’yiwuwar idan an wanzar da zaman lafiya bangarorin biyu za su samu damar tsira da mutuncinsu, wanda kuma hakan zai bai wa yankinmu damar fita daga ukubar da aka jefa shi ciki.’’

Turkiyya na sane da yadda kungiyoyin ta’addanci ke "amfani da kalamai da diflomassiya da dabarun soji", in ji Erdogan ya na tabbatar da cewa kasarsa na bin su abin da suke yi sau da kafa.

Ya kara da cewa "kamar yadda ba mu yarda a yi wa kasarmu kawanya da wata hanyar ta'addanci ba, tabbas ba za mu bari a sake yin wani yunkuri ko dabara ba."

Dangane da harin baya-bayan nan da aka kai kan littafin Alkur'ani mai tsarki na Musulmai a kasashen Turai, Erdogan ya ce hakan ba abu ne da za a amince da shi ba, ya kuma ce: "Wannan laifi ne da ke nuna kiyayya a fili."

"(Ganganci ne kona Al-Kur'ani) wannan ta'asa ce da ba wai al’ummar Musulmai kusan miliyan biyu kawai aka bata wa rai ba, abu ne da ka iya tunzura su, kuma wannan yanayi ne da dole a kawo karshen shi nan take," in ji shi.

TRT World