Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce "dimokuradiyyar Turkiyya da kasar" ne suka yi nasara a zaben da aka yi a karshen mako duk da yadda sakamakonsa ya kasance.
“Muna biyayya ga matakin da 'yan kasa suka dauka ta hanyar zabe," in ji Erdogan a sakon da ya wallafa a Twitter ranar Litinin game da zaben ranar 14 ga watan Mayu.
Ya ce yana da yakinin cewa kawancensa na siyasa zai yi nasara ta hanyar samun karin kuri'u ranar 28 ga watan Mayu idan aka je zagaye na biyu, yana mai karawa da cewa: “ina sa ran za mu samu nasara ta tarihi.”
Al'ummar Turkiyya sun "jaddada amincewarsu da imaninsu a kan kawancenmu" ta hanyar zaben Kawancen Al'umma da mafi rinjayen kuri'u a majalisar dokokin kasar.
Tun da farko ranar Litinin, Hukumar Koli ta Zaben kasar ta ce za a je zagaye na biyu na zaen Turkiyya ranar 28 ga watan Mayu bayan an rasa dan takarar da ya samu isassun kuri'un da za su ba shi damar yin nasara a zaben Lahadi.
A zagayen na farko babu dan takarar da ya samu kashi 50, amma Erdogan ne yake kan gaba da kashi 49.51 na kuri'un da aka kada, a cewar Ahmet Yener, shugaban Hukumar Koli ta Zaben kasar (YSK).
Karin bayani: Za a je zagaye na biyu na zaben Turkiyya na 2023
Mai biye masa shi ne shugaban babbar jam'iyyar hamayya ta Republican People's Party (CHP) Kemal Kilicdaroglu, wanda ke takara a kawancen jam'iyyu shida da ake kira Kawancen 'Yan Kasa, wanda ya samu kashi 44.88.
Yanzu dai su biyu ne za su fafata ranar 28 ga watan Mayu.
Kazalika, Sinan Ogan na Kawancen Ata ya samu kashi 5.17, shi kuma Muharrem Ince, wanda ya janye daga takarar a karshen makon jiya bayan an buga takardun jefa kuri'a, ya samu kashi 0.44, in ji Yener.
Kashi 88.92 na masu zaben sun jefa kuri'a a cikin kasar, yayin da kashi 52.69 suka yi zabe a kasashen waje, a cewar Yener. Ana cigaba da tattara kuri'u 35,874 da aka kada daga masu jefa kuri'a na kasashen waje, in ji shi.
Karanta karin labari mai alaka: Kai-tsaye: Bayanai kan zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin Turkiyya