Atasever zai kasance a cikin jirgin a bulaguron jirgin na ƙarshe. / Hoto: AA

Dan sama jannati na biyu na Turkiyya Tuva Cihangir Atasever, zai kasance a cikin jirgin bincike na VSS Unity na kamfanin Virgin Galactic da zai zagaye sararin duniya a ranar Asabar, wanda zai tashi daga jihar New Mexico ta Amurka, a bulaguro na ƙarsh da jirgin zai yi.

Jirgin na VSS Unity yana ɗauke da matuƙa biyu, sannan yana da na'urorin da za su ba shi damar sauka a duniyarmu ta Earth bayan harab shi sararin samaniya, inda gudunsa zai wuce na ƙara sau uku a cikin minti ɗaya, da kuma nisan fiye da kilomita 15 daga sararin duniya.

An fara harba jirgin sararin samaniya ne a watan Disamban 2018, sai kuma a watan Yulin 2021 ya fara tafiya da mutane, kafin daga bisani a mayar da shi jirgin ɗaukar fasinja a watan Yulin 2023.

Atasever zai kasance a cikin jirgin a bulaguron jirgin na ƙarshe.

A watan Mayu ne Kamfanin Virgin Galactic ya sanar da cewa ya buɗe sabuwar tasha a Kudancin California don samar da sabon samfurin jirgin sama jannati na Delta, wanda zai iya zagaye sau takwas a sararin saaniya cikin wata ɗaya.

Tafiyar da ɗan sama jannati Atasever zai yi da jirgin Virgin Galactic na zuwa ne bayan bulaguron ɗan sama jannatin Turkiyya na farko a watan Janairu zuwa Tashar Ƙasa da Ƙasa ta Sararin Samaniya a shirin Axiom Mission 3 mission.

TRT World