An bayar da kambi na kasa a Burkina Faso ga shugaban zartarwar kamfanin Baykar na Turkiyya mai samar da jiragen yaki marasa matuka samfurin Bayraktar TB2 da aka fitar zuwa kasar.
A ranar Talatar nan ne Haluk Bayraktar ya karbi lambar girma ta kasa ta ‘Ordre de L'etalon Officier’, kambi mafi girma a Burkina Faso wanda shugaban kasar Ibrahim Traore ya bayar da umarnin ba shi, saboda gudunmowar musamman da yake bayarwa wajen dabbaka zaman lafiya a Yammacin Afirka.
Babban Sakataren gwamnatin Burkina Faso Andre Roch Compaore ne ya mika kambin girmamawar ga Bayraktar a yayin wani biki da aka gudanar a babban birnin kasar Ouagadougou.
Daga baya Byraktar ya gana da shugaban kasar wanda ya gode masa bisa wannan gudunmowa da yake bayarwa.
Jiragen yaki marasa matuka samfurin Bayraktar TB2 ne mafi shahara daga kayan tsaro na kamfanin Baykar, wanda kuma suka taka rawar gwani a rikicin Libiya da Karabakh da ma Yukren a baya-bayan nan.
Gamayyar Masu Fitar da Kaya daga Turkiyya ta sanar da cewar a 2021, Baykar ne a kan gaba cikin kayan tsaro da aka fitar zuwa kasashen waje daga Turkiyya.
Baykar da ya fitar da kaso 99.3 na kayayyakin da ya kulla yarjejeniyar zai fitar a 2022, ya samu kudi har dalar Amurka biliyan 1.18.