Ana zaben shugaban Turkiyya ne ta hanyoyi biyu inda da farko dole ya samu fiye da kasha 50 na kuri’un da aka kada a dukka fadin kasar /Hoto: AA

Za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin Turkiyya ranar 14 ga watan Mayu, inda jam’iyyar AK ta Shugaba Recep Tayyip Erdogan take neman yin ta-zarce.

Jam’iyyar hamayya ta CHP ta tsayar da shugabanta Kemal Kilicdaroglu a matsayin dan takarar shugaban kasa.

Yaya ake gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dokokin kasar?

Zaben shugaban kasa

A watan Yulin 2018, an rantsar da Shugaba Erdogan a matsayin shugaban kasa karo na biyu, inda Turkiyya ta sauya daga tsarin ‘yan majalisar dokokin zuwa na shugaba mai cikakken iko.

Ana zaben shugaban Turkiyya ne ta hanyoyi biyu inda da farko dole ya samu fiye da kashi 50 na kuri’un da aka kada a duk fadin kasar.

Idan bai samu wannan adadi na kuri’u a zagayen farko ba, za a je zagaye na biyu tsakanin ‘yan takara biyu da suka fi yawan kuri’a a zaben farko.

Sharuddan zama dan takarar shugaban kasa sun hada da cewa, dole mutum ya zama dan kasar Turkiyya da ke da akalla shekara 40 a duniya kuma ya kammala karatun digiri a kowanne bagare.

Duk jam’iyyar da ta yi nasara da kashi biyar cikin 100 na kuri’un da aka jefa a zaben majalisar dokokin da ya gabata za ta iya tsayar da dan takara. Kazalika idan jam’iyyu suka yi kawance sannan suka samu wannan adadi, za su iya tsayar da dan takarar gamayya.

Haka kuma ‘yan takara masu zaman kansu suna iya tsayawa takarar shugaban kasa idan mutum 100,000 da suka yi rajistar zabe suka amince da hakan.

Za a sanya sunayen ‘yan takara da jam’iyyunsu da hotunansu a takardar kuri’ar zaben shugaban kasa. Masu zabe za su dangwala a kan “e” wato evet a harshen Turkanci kan dan takarar da suke so.

Da yake mutane ne kai tsaye suke zabar shugaban kasa, ba za a iya cire shi daga kujerarsa kafin wa’adinsa ya kare ba.

A matsayinsa na shugaban kasa, yana da iko ta fannoni daban-daban da kundin tsarin mulki ya ba shi.

Sun hada da yin dokoki da nada mataimaka da minsitoci da manyan jamian gwamnati da sanarwa da sanya hannu a yarjejeniyoyin kasa da kasa da tsara manufofin kasashen waje dan kuma tsara manufofin tsaron kasa.

Shugaban Jam'iyyar AK Recep Tayyip Erdogan shi ne shugaban kasar Turkiyya mai ci kuma yana neman karin wa'adi a zaben watan Mayu/ Hoto: AA

Zabukan Majalisar Dokoki

Turkiyya za ta gudanar da zabukan da za a zabi ‘yan Mjalisar Dokokin kasar 600 – na Majalisar Dattijai da ta Wakilai, da za su wakilci gundumomi 87 da larduna 81.

An ware wa gundumomi kujerun majalisa daidai da yawan al’ummominsu. A misali, Istanbul na da ‘yan majalisar dokoki 98 yayin da Ankara ke da 36 a dukkan gundumomi uku-uku da suke da su.

Yayin da yankuna mafi girma na uku da na hudu Izmir da Bursa ke da gundumomi bibbiyu.

Domin cike gurbin wadannan kujeru, ‘yan Turkiyya za su zabi jam’iyya daya da ‘yan takararta da aka tantance daga wadannan gundumomin.

Domin samun rinjaye, dole ne jam’iyya ta samu fiye da rabin kujerun majalisar dokokin – 301.

Domin cancantar samun kujeru a majalisa, dole ne jam’iyya ta samu kashi bakwai na sahihan kuri’un da aka kada a fadin kasar a karan kansu ko kuma ta hanyar yin kawance da wasu jam’iyyun.

Sai dai wannan tsarin bai shafi ‘yan takara masu zaman kansu ba.

A ranar zabe, masu kada kuri’a za su dangwalawa “e” wato “evet” – a kan takardar da ke dauke da sunaye da alamun jam’iyyun da ke takara a zaben. Idan jam’iyyu suka yi gamayya kafin zabe, za a sanya sunan gamayyar a kan takardar kuri’ar.

Ana gudanar da kidayar kuri’u ne ta wani salon lissafi da ake kira da tsarin D'Hondt, wanda ake amfani da shi a kasashe da dama da suka hada da Belgium da Brazil da Denmark da Japan da Switzerland, tare da tabbatar da cewa an bai wa jam’iyyu kujeru daidai yawan kuri’un da suka samu.

Rawar da Hukumar Zabe ta Koli ke takawa

Bayan an kammala kirga dukkan kuri’u, Hukumar Zabe ta Koli (YSK) na sanar da sakamako a fadin kasar.

YSK, Hukumar Zabe mafi girma a Turkiyya na da alhakin daukar dukkan matakan tabbatar da adalci da sanya idanu tun daga farko har zuwa karshen zaben /Hoto: AA

YSK, Hukumar Zabe mafi girma a Turkiyya na da alhakin daukar dukkan matakan tabbatar da adalci da sanya idanu tun daga farko har zuwa karshen zaben.

Hukumar na da mambobi bakwai manya da kuma wasu hudu da suke zaune a benchi don maye gurbin wani idan bukatar hakan ta taso.

Baya ga sanya idanu da kula da yadda zabe ya gudana a dukkan fadin kasar, Hukumar na da alhakin rejistar zabe ga ‘yan kasar Turkiyya da ke zaune a kasashen ketare.

Hukumar ce ke da cikakken ikon yanke matakin karshe kan duk wata matsala da aka samu a lokaci ko bayan kammala zabe.

TRT World