Tare da gwamnatocin hadaka a shekarun 1979 da 1990, an samu rashin tabbas da daidaito a siyasar Turkiyya, wanda hakan ya dinga janyo sojoji na kifar da zababbu suna karbe mulki.
Gwamnatocin hadaka suna gaza cimma matsaya wanda hakan ke janyo samun tsaiko wajen gudanar da gwamnati.
A shekarar 2017 bayan yunkurin juyin mulkin da aka yi a shekarar da ta gabace ta, Turkiyya karkashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan ta yi kokarin sauya tsarin shugabanci daga mai amfani da firaminista zuwa mai amfani da shugaban kasa mai cikakken iko.
Erdogan ya bayyana sabon tsarin a matsayin tsarin shugabanci irin na Turkiyya, inda yake da amannar wannan tsarin zai ja hankalin wasu kasashen duniya.
A ranar 14 ga Mayu Turkiyya za ta gudanar da sabbin zabuka, na shugaban kasa da ‘yan majalisar dokoki.
A lokacin da wasu masana kimiyyar siyasa ke kallon Faransa a matsayin mai aiki da tsarin shugaban kasa rabi-da-rabi, Amurka kuma ita ce mai cikakken misalin tsarin shugaban kasa.
Ga dai misali mai sauki wajen kwatanta tsarin shugabancin kasar Turkiyya da na kasashen Faransa da Amurka:
Zabukan Shugaban Kasa
A Turkiyya da Faransa ana iya gudanar da zaben shugaban kasa har zagaye biyu, sabanin a Amurka da ake zabar shugaba a zabe guda daya kawai.
A Faransa da Amurka ana gudanar da zabukan ‘yan majalisar dokoki a lokaci daban da na zaben shugaban kasa, inda a Turkiyya ake yin zabukan nasu a lokaci guda.
Ofis din Firaminista
Kamar yadda yake a Amurka, babu ofishin Firaminista a tsarin shugaban kasa na Turkiyya. A yayin da shugaban kasar Turkiyya zai iya nada mambobin majalisar gudanarwa kai tsaye, shugaban kasar Amurka zai iya nada ministoci ne bayan amincewar majalisar dokokin kasar.
Sakamakon haka, a Turkiyya da Amurka, shugaban kasa na da cikakken ikon nada duk wadanda za su jagoranci hukumomin gwamnati, daga manufofin harkokin kasashen waje zuwa yanke hukunce-hukunce kan al’amuran cikin gida da tattalin arziki.
A Faransa, ana bai wa shugaban kasa damar nada ministocin tsaro da harkokin waje, amma harkokin cikin gida da tattalin arziki na hannun ikon Firaminista, wanda ke da alhakin nada ministocin majalisar zartarwa.
Hakan ya sanya ake kiran tsarin Faransa na shugaban kasa na rabi-da-rabi, ba kamar na Amurka da shugaba ke da cikakken iko ba.
Tsarin shugaban kasa na rabi-da-rabi na nuni da wasu kamanceceniya da na shugabancin majalisa, wanda kasashe irin su Ingila da Jamus da wasun su da yawa a Yammacin duniya ke amfani da shi.
Amma shugaban kasa na tsarin rabi-da-rabi na da karfin iko da ba a saba gani ba a tsarin da ke amfani da Firaminista, madalla da tsarin da ya bayar da dama inda mafi yawan jama’a ke zabar su.
A yayin da shugabannin kasa ke zama shugabannin gwamnati a tsarin gudanarwa mai aiki da Firaminista, a karkashin tsarin kuma majalisun dokoki ne suke zabar su.
Sakamakon yadda ba su da halaccin kuri’u mafiya rinjaye, ofishin shugaban kasa a tsarin amfani da Firaminista ya kan zama na je-ka-na-yi-ka kan batun gudanarwa.
Ikon rushe majalisar dokoki
Game da batun rushe majalisar dokoki, tsarin shugaban kasar Turkiyya ya sha bam-bam da na Amurka.
A yayin da shugaban kasa a Turkiyya ke da ikon rushe majalisar dokoki, a Amurka abun ba haka yake ba inda shugaban kasa ba shi da ikon rushe majalisar dattawa ko ta wakilai.
A wannan yanayi, tsarin Turkiyya daidai yake da na Faransa wanda shugaban kasa ke da ikon rushe majalisar dokoki a duk lokacin da ya so, bayan tuntubar Firaminista da shugabannin majalisun dokokin biyu
Tsige shugaban kasa
Game da tsige shugaban kasa daga kan kujerarsa kuwa, tsarin Turkiyya na kamanceceniya sosai da na Amurka sama da na Faransa.
A Amurka, Majalisar Dokoki na da ikon tsige shugaban kasa idan masu son hakan suna da rinjaye, amma dole ne sai kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar dattawa sun amince da hakan sannan za a iya tsige shi.
A Turkiyya kuma, majalisar dokokin Turkiyya na iya kira da a gudanar da sabon zaben shugaban kasa idan kashi uku cikin biyar na ‘yan majalisar suka amince da hakan.
A Faransa, ana iya tsige shugaban kasa ne bayan an samu rinjaye dan kadan a dukkan majalisun dokoki, ba kamar a tsarin Turkiyya da Amurka ba, wanda ke bukatar rinjaye da yawa – na biyu bisa uku ko uku bisa biyar.
Idan dukkan majalisun dokoki suka amince da su tsige shugaban kasar Faransa, sashe na 68 na kundin tsarin mulki ya tanadi cewar Majalisar Dokoki da ke zama a matsayin babbar kotu ce kadai za ta iya yin hakan.
Kira ga gudanar da kuri’ar raba gardama
Ba kamar a tsarin Amurka ba, wanda ba shi da neman a kira ga kuri’ar raba gardama a matakin Tarayya, tsarin shugabancin kasa na Turkiyya da Faransa ya bayar da wannan dama a matakin kasa kan muhimman batutuwa da suka shafi kundin tsarin mulki.
A matakin jihohi, Faransa da jihohin Amurka 23 sun bayar da damar za a iya kiran da a yi kuri’ar raba gardama a kan batutuwa daban-daban, amma tsarin shugaban kasa na Turkiyya ba shi da wannan tanadin.
A Faransa, shugaban kasa zai iya yin kira da a gudanar da kuri’ar raba gardama kan kowanne irin batu.
Haka kuma kundin tsarin mulki ya ba shi damar zai iya kira ga kuri’ar raba gardamar idan majalisar dokoki ko majalisar ministoci ta bayar da umarnin a yi hakan.
A karshe, a Faransa kashi daya cikin biyar na ‘yan majalisar dokoki na da ikon kira da a gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a, amma sai sun samu goyon bayan daya cikin goma na masu jefa kuri’a, kan batutuwan da suka shafi dokokin gwamnati da yadda hukumomin gwamnati za su yi aiki.
A gefe guda kuma, shugaban kasa na iya kiran da a gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a game da wani canji da za a yi a kundin tarin mulki.
Sannan idan a Turkiyya wata doka ba ta samu adadin ‘yan majalisar dokoki da za su amince a ita ba, to ana yin kiran da a gudanar da kuri’ar raba gardama ba tare da tsoma bakin shugaban kasa ba.
Kuri’ar raba gardama na taka rawa sosai a siyasar Turkiyya da Faransa.
A 2017 ne aka gudanar da kuri’ar raba gardama da ta sauya tsarin shugabancin Turkiyya daga na firaminista zuwa na shugaban kasa.
Haka zalika a 1958 ne aka amince da tsarin shugaban kasa na rabi-da-rabi bayan kuri’ar raba gardamar da aka jefa.
A 1992 ne aka gudanar da kuri’ar raba gardama ta Yarjejeniyar Maastricht don bai wa Faransa damar shiga Tarayyar Turai.
Nada jakadu
A yadda abun yake a Amurka shi ne, shugaban kasa zai nada jakadu tare da samun shawarwari daga majalisar dattawa, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Saboda haka, sai majalisar dattawa ta amince da mutum sannan zai zama jakadan Amurka a wata kasa.