Bankin ya dauki matakin ne kasa da wata daya bayan ya nada ministan kudi . / Hoto: Reuters Archive

Babban Bankin Turkiyya ya kara kudin ruwa daga kashi 8.5 zuwa kashi 15 ranar Alhamis.

Bayan zabukan da aka yi a watan Mayu, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya nada Mehmet Simsek a matsayin sabon Ministan Kudi da Baitulmali sannan ya bai wa fitacciyar ma'aikaciyar banki Hafize Gaye Erkan mukamin Gwamna ta Babban Bankin kasar.

“Kwamitin ya yanke shawarar soma daukar matakan matse harkokin kudi domin rage hauhawar farashi nan ba da jimawa ba, da kuma kauce wa yiwuwar karuwar hauhawar farashi da ma rage tsarin hawan farashi,” in ji bankin.

“A yayin da hauhawar farashi a duniya take raguwa, duk da haka ta wuce yadda ya kamata ta kasance a tsaka-tsaki. Don haka, manyan bankuna a fadin duniya suna ci gaba da daukar matakai na rage hauhawar farashi.”

Bankin ya dauki matakin ne kasa da wata daya bayan ya nada ministan kudi, wanda a baya ya sha jaddada bukatar yin garanbawul kan tsare-tsaren kudi.

“Kwamitin zai yanke shawara kan fasalin harkokin kudi ta yadda za a kirkiro hanyoyin kudi da za su tabbatar da raguwar hauhawar farashi sannan hauhawar ta kai kashi 5 a matakin matsakaicin zango,” a cewar sanarwar.

“Daukin matakin matsi kan harkokin kudi zai karfafa hanyoyin rage hauhawar farashi a kan lokaci.”

TRT World