Babu wani abu da zai maye gurbin yarjejeniyar jigilar hatsi ta Bahar Aswad, in ji Akif Cagatay Kilic, babban mai bayar da shawara ga shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
Da yake bayyana muhimmancin dawo da yarjejeniyar jigilar hatsin, Kilic ya ce “wannan ne abun da muka bai wa fifiko. Don haka, ba ma so a maye gurbinta da wani abu daban.”
Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai ziyarci Rasha ‘nan ba da jimawa ba’ don tattaunawa da Putin, kamar yadda mai magana da yawun Jam’iyyar AK Omer Celik ya shaida wa manema labarai.
Ya ce za a gudanar da ganawar ne a garin Sochi na yawon bude ido da ke Rasha, inda ya kara da cewar Turkiyya na son kawar da hatsarin rikicin karancin abinci da za a iya samu.
A ranar 17 ga Yuli ne Rasha ta jingine aiki da yarjejeniyar jigilar hatsi ta Bahar Aswad wadda Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya suka jagoranci kullawa don dawo da jigilar hatsi daga tashoshin jiragen ruwa uku na Yukren, wanda aka dakatar bayan fara yakin Rasha da Yukren a watan Fabrairun 2022.
Moscow na nanata korafi cewa kasashen Yammacin duniya ba su cika nasu bangaren na yarjejeniyar ba. Kuma hana biyan kudade da samun kayan aiki da inshora na janyo tsaiko ga jigila a teku da take yi don shiga ko fitar da kayayyaki.
Ankara kuma na ta yin kokarin ganin an dawo da aiki da yarjejeniyar da aka kulla a watan Yulin 2022, ta kuma yi kira ga Kiev da Moscow su kawo karshen yakin da suke yi.