Waƙar tana ɗauke da hotunan AI da ke nuna yain Gaza, da kuma wasu ainihin bidiyo daban-daban daga yakin da aka yi ƙawaya.

A wani lamari mai ban sha'awa da nuna haɗin kai ga Falasdinu, ɗan Majalisar Dokokin Turkiyya Yucel Arzen Haciogullari ya fitar da wata waƙa ta mutum-mutumi (AI) mai suna ''Ƙauracewa'', inda ya buƙaci masu saurare kan su ɗauki mataki klan yakin da Isra'ila ke yi a Gaza.

Waƙar, wacce Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya wallafa a ranar Litinin, ta bayyana wasu hotuna masu ratsa jiki kan irin wahalhalun da mutanen da ba su ji ba su kuma gani ba suke fuskanta a yankin da ake yi wa ƙawanya, inda aka nuna yadda ''Jariri ya mutu ba tare wata alama ba, ya tafi cikin zalunci.''

Erdogan, wanda ya wallafa wakar a shafin X, ya rubuta cewa: ''Muna tare da Gaza da 'yan'uwanmu Falasdinawa da muryoyinmu da harsunanmu da addu'o'inmu da taimakon jinƙai da kuma duk hanyoyin da za mu iya.''

Ya kuma ƙara da cewa ''Turkiyya za ta ci gaba da ba da goyon bayanta tare da yin tsayin daka.''

Waƙar ta ƙarfafa wa masu sauraro kan su ci gaba da jajircewa a yaƙin da suke yi na samar da adalci: ''Yaya za mu yi? Bugu da bugun jini. Ta yaya za mu yi yaƙi? Manufa kan manufa.''

''Ƙauracewa, za ta sanya mu iya rike ƙasarmu,'' in ji waƙar, tana mai nuni kan mamayar da sojojin Isra'ila suka yi wa yankunan Falasdinawa da kuma haɗarin da ke tattare da yiwuwar yaduwar rikicin a yakin baki ɗaya.

Tallafin Turkiyya ga Falasdinu

Fahrettin Altun, Daraktan Sadarwa na Turkiyya, ya kuma jaddada goyon bayan Turkiyya ga Falasdinu ta hanyar yada wakar a shafukansa na sada zumunta.

"Za a ci gaba da gwagwarmayarmu har sai Falasdinu ta samu cikakken 'yanci," kamar yadda Altun ya jaddada a cikin sakon tare da bidiyon.

''Turkiyya za ta ci gaba da aiki tare da koƙarin kare hakkin 'yan'uwanta Falasdinawa da kuma tallafa musu ta kowane fanni, za mu ɗauki dukkan matakan da suka kamata domin kawo ƙarshen dabi'ar Isra'ila ta rashin bin doka.'' in ji shi.

Mai magana da yawun jam'iyyar AK Omer Celik, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na intanet, ya saɗaukar da waƙar zuwa ga adalci da girmamawa da kuma mutunta ɗan adam tare da kare hakkokin jarirai da mata - musamman ga Gaza.

Turkiyya dai ta kasance kan gaba wajen sukar zaluncin da Isra'ila ke yi kan Falasdinawa a Gaza da kewanyanta, ciki har da mamaye matsugunan da ba bisa ka'ida ba a Yammacin Gabar Kogin Jordan da kuma sanya shinge a tattalin arzikin yakin da ta shafe tsawon shekaru tana yi.

Bayan farmakin da Isra'ila ta kai a watan Oktoba bara, Turkiyya ta kara zafafa adawarta , inda ta yi amfani da wasu hanyoyin wajen yin ƙira ga ƙasashen duniya su ba da haɗin kai da kuma shiga tsakani kan mumunar zaluncin Tel Aviv.

Haka kuma, Ankara tana kan bin shari'ar da ake yi a kotun duniya (ICJ) inda aka zargi Isra'ila da aikata kisan kiyashi kan Falasdinawa. Haka kuma ta dakatar da huldar kasuwanci da Isra'ila.

Tun lokacin da Isra'ila ta fara kai hare-hare kan Gaza, duniya ta yi ta kauracewa kayayyakin da Isra'ila ke yi a duniya.

TRT World