Sumela Monastery na daya daga cikin wurare 21 a Turkiyya da aka jera cikin wuraren tarihi na UNESCO, yana da nisan mita 300 a saman dazuzzukan da suka mamaye kwarin Altindere a lardin Trabzon na arewa maso gabashin kasar. Hoto: Taskar AA      

An zabi Turkiyya a matsayin mamba a kwamitin adana kayan tarihi na Hukumar Raya Ilimi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO a wa'adin shekarar 2023 zuwa 2027.

An gudanar da zaben ne a ranar Laraba a babban taron kasashe mambobin da ke cikin kwamitin adana kayayyakin tarihi na duniya karo na 24 a birnin Paris.

Turkiyya ta samu nasara da adadi mafi yawa na kuri'u 137 a bangaren kujerar neman matsayin da ya rage a kwamitin.

Kasar ta taba aiki a kwamitin har sau biyu a shekarun 1983 zuwa 1989 da kuma shekarar 2013 zuwa 2017.

A cewar ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya, ''kasar tana da burin amfani da gogewarta da ilimin da ta tara wajen gudanar da ayyuka da kare wurare 21 na kayayyakin tarihi a duniya da ke wakiltar duk wani ci-gaba da ya taba wanzuwa a yankin Anatolia tun zamanin da aka samu a fasaha tsakanin dan'adam kafin tarihi da aka fi sani da Neolithic, a ayyukanta da ta yi a duniya a matsayin mamba ta kwamitin UNESCO."

Kwamitin tarihi na UNESCO, wanda ke da alhakin inganta al'adu da albarkatun kasa tare da tarihi a duniya wadanda ake la'akari da su a matsayin abubuwan da aka yi gadonsu kana kwamitin yana gudanar da ayyukan da suka shafi jerin abubuwan tarihi na duniya, inda wurare 21 daga Turkiyya suke daga ciki.

TRT World