Fidan ya jadada gagarumin ci gaba da aka samu a tattaunawar zaman lafiya, tare da ganin an kai ga cimma matsaya ta hadin gwiwa kuma mai inganci. / Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana a ranar Talata cewa Habasha da Somalia sun samu gagarumin ci gaba wajen kawar da sabanin da ke tsakaninsu kan yarjejeniyar tashar jiragen ruwa da Addis Ababa da yankin Somaliland suka cimma a farkon wannan shekara.

"Na yi farin cikin sanar da cewa adadin da kuma girman batutuwan da muka tattauna sun ƙaru sosai idan aka kwatanta da zagayen farko," in ji Fidan a wani taron manema labarai, tare da rakiyar Ministan Harkokin Wajen Somalia Ahmed Moalim Fiqi da Ministan Harkokin Wajen Habasha Taye Atske Selassie Amde.

Shirin "Ankara" na neman kwantar da tarzoma tsakanin kasashen da ke makwabtaka da gabashin Afirka.

Fidan ta ce bangarorin biyu sun amince da muhimman ƙa'idoji, wadanda za su taimaka a tattaunawar da za a yi nan gaba.

"Za mu sake taro a Ankara ranar 17 ga watan Satumba a zagaye na uku, tare da fatan samun nasarar kammala wannan aiki."

A farkon watan Yuli ne ministocin harkokin wajen Habasha da Somaliya suka gudanar da tattaunawar farko ta kai tsaye a Ankara babban birnin kasar Turkiyya.

Tashin hankali kan yarjejeniyar tashar jiragen ruwa

Habasha, kasa mafi yawan jama'a a duniya da ba ta da teku, ta rasa hanya tsakaninta da teku bayan samun 'yancin kai na Eritrea a 1991.

Samun damar shiga Tekun Bahar Maliya ya kasance muhimmin batu na tattalin arziki ga Habasha. Takaddama tsakanin Somaliya da Habasha ta kaure tun bayan da Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da yankin da ke ballewa na Somaliland a watan Janairu.

Yarjejeniyar ta bai wa Habasha damar shiga tekun ta Somaliland, sannan kuma Habasha za ta amince da Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Sanarwar ta haifar da koma baya sosai daga Somalia, inda ta yi Allah wadai da ita a matsayin cin zarafi ga 'yancin kanta da kuma yankinta. Somaliland yanki ne da ya balle daga Somaliya kuma ba a amince da shi a duniya ba.

A ranar 8 ga Mayu, 2024, jakada na musamman na firaministan Habasha, Mulatu Teshome Wirtu, tare da rakiyar Ministan Harkokin Wajen Habasha, ya samu tarba daga shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

A yayin ganawar, Habasha ta nemi goyon bayan Turkiyya game da rikicinta da Somaliya. A matsayin amintacciyar mai shiga tsakani, Turkiyya ta fara kokarin shiga tsakani bisa umarnin Shugaba Erdogan.

Kasashen duniya sun yaba da kokarin da Turkiyya ke yi na kafa hanyar tattaunawa mai ɗorewa a tsakanin bangarorin a daidai lokacin da ake samun tashe-tashen hankula a wasu sassan yankin.

TRT World