Jirgin SpaceX Dragon Capsule Freedom mai ɗauke da ma'aikatan Axiom Mission 3 (Ax-3), ciki har da ɗan sama jannatin Turkiyya na farko Alper Gezeravci, ya dawo duniya cikin nasara inda ya sauka a Gaɓar Tekun Florida, bayan zamansu na kwanaki 18 a tashar sararin samaniya ta kasa da kasa (ISS).
Kumbon ya bar jikin tashar ISS a ranar Laraba kuma ya fara bulaguron komawa duniya.
Tsarin dawowar ya ɗauki kusan awa 47 inda tafiyar ta kawo ƙarshe a ranar Juma'a, lokacin da jirgin ya gangara kan teku. Tawagar da ke jiran isarsa ta kwaso matafiyan cikin gaggawa daga cikinsa.
Tawagar da ke cikin jirgin na Ax-3 na Turai sun haɗa da babban ɗan sama jannati na Axiom Space da tsohon kwamandan ISS Michael Lopez-Alegria, wanda ke wakiltar Spain da Amurka a matsayin kwamandan tawagar Ax-3. A shekarar 2022, ya jagoranci Axiom Mission 1 (Ax-1), a tafiya ta farko ta ƙashin kai da ISS.
Matukin jirgin shi ne Kanar Walter Villadei daga Rundunar Sojan Sama ta Italiya. Gezeravci, matukin jirgin saman F-16, yana shiga cikin Ax-3 a matsayin ƙwararre a harkar, tare da ɗan sama jannatin Sweden Marcus Wandt daga Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Turai.
An harba jirgin Ax-3 ne daga cibiyar binciken sararin samaniya ta NASA ta Kennedy da ke Florida a ranar 19 ga watan Janairu, a kan wata roka kirar SpaceX Falcon 9.
Tawagar da ke cikinsa sun tsaya a tashar sararin samaniya ta ƙasa da ƙasa a washegarin ranar 20 ga Janairu.
A tsawon sama da mako biyu da suka yi a tashar, matukin jirgin saman Turkiyya Kanar Alper Gezeravci tare da ma'aikatansa uku daga Spain da Italiya da Sweden sun gudanar da gwaje-gwajen kimiyya sama da 30, kusan rabinsu na Gezeravci da kansa.
An dage dawowar ma'aikatan jirgin sau da yawa saboda rashin kyawun yanayi.