Titin Ataturk an rufe shi sakamakon cunkoson ababen hawa biyo bayan tashin bam din wanda ke kusa da daya daga cikin kofofin shigar Babbar Majalisar Kasar. Hoto/ AA

Akalla ‘yan sanda biyu aka raunata a lokacin da wasu ‘yan ta’adda suka tayar da bam a gaban Babban Ofishin Tsaron Turkiyya da ke Ma'aikatar Cikin Gida a Ankara, inda daya daga cikin ‘yan ta’addan ya kashe kansa da bam din.

“’Yan ta’adda biyu, wadanda suka zo a wata karamar motar haya a gaban kofar shiga Babban Ofishin Tsaro, sun kaddamar da harin ta’addanci.

Daya daga cikinsu ya kashe kansa,” kamar yadda Ali Yerlikaya ya bayyana a ranar Lahadi. Yerlikaya ya bayyana cewa an ji wa ‘yan sanda biyu ciwo a yayin harin duk da cewa ciwon ba mai tsanani bane.

Harin ya faru da misalin karfe 9:30 na safe, wato 0630 agogon GMT. An ji karar harin a gaban Ma’aikatar Cikin Gida ta Turkiyya wadda ke a tsakiyar Ankara.

Bayan karar bam din da harbe-harben bindiga da aka ji kusa da ginin ma’aikatar da ke Kizlay, wanda shi ne babban wuri a birnin da ke gundumar Cankay, ‘yan sanda sun kara tsaurara tsaro a wurin.

Titin Ataturk an rufe shi sakamakon cunkoson ababen hawa biyo bayan tashin bam din wanda ke kusa da daya daga cikin kofofin shigar Babbar Majalisar Kasar.

An tura ‘yan sanda na musamman zuwa wurin da lamarin ya faru. Haka jami’an kashe gobara da kuma likitoci sun isa wurin.

Two terrorists detonated a bomb in front of the General Directorate of Security in the Turkish capital of Ankara.

Za a bude Babbar Majalisar kasar da rana bayan shafe hutun watanni uku.

Ofishin Babban Mai Shigar da Kara na Ankara ya kaddamar da bincike kan harin na ta’addanci.

TRT World