An buɗe taron diflomasiyya na Antalya (ADF) a birnin Antalya da ke gaɓar Tekun Bahar Rum na ƙasar Turkiyya, inda zai karɓi baƙuncin wakilai daga ƙasashe 147 ƙarƙashin taken "Daukaka Diflomasiyya a yayin rikice-rikice."
Kusan mahalarta 4,500 da suka haɗa da shugabannin ƙasashe 19 da ministoci 73, da wakilan ƙasashe 57 ne ake sa ran za su halarci taron karo na uku da aka fara ranar Juma'a.
Taron zai ƙunshi mahalarta da dama, daga jami'an diflomasiyya da ƴan siyasa zuwa ɗalibai da malamai da ƙungiyoyin farar-hula da kuma ƴan kasuwa.
Taron zai tattauna batutuwa na duniya daban-daban kamar matsalar sauyin yanayi da ƙaura da ƙyamar Musulunci da rikicin fagen kasuwanci, da kuma batun ƙirƙirarriyar basira.
Za a gabatar da ƙananan taruka fiye da 50 a yayin babban taron daga tsakanin 1 ga Maris zuwa 3 ga Maris, sannan kuma za a baje-kolin abubuwa da yawa.
Za a buɗe baje-kolin Ƙarnin Turkiyya a wajen taron, wanda zai nuna abubuwan da Turkiyya ta sa a gaba a fannin fasaha da makamashi da tsaro da kuma masana'antu.
Har ila yau taron zai haɗa da nuna shirin "Bulletproof Dreams: Gaza Children Painters Exhibition", wato Nunin zanen Yara na Gaza, wanda Sashen Sadarwa na Fadar Shugaban Ƙasar Turkiyya ya shirya domin bayyana matsalolin jinƙai da yara ke fuskanta a Gaza.
Batutuwan da za a tattauna daga yankin Balkan zuwa al'amuran Afirka
Bayan buɗe taron, za a gudanar da wani kwamitin shugabanni mai taken 'Daukaka Diflomasiyya A yayin rikice-rikice', wanda ke ɗauke da sunan taken taron na bana.
Kwamitin, wanda ya ƙunshi shugabannin ƙasashen Bulgaria da Kosovo da Somalia da Djibouti, zai tattauna kan ci-gaba da ba da haske kan harkokin diflomasiyya.
Kwamitin na biyu zai tattauna kan inganta ra'ayin jama'a a lokacin rikici, wanda zai ƙunshi shugabannin Madagascar da Guinea-Bissau da Kongo.
Taron zai haɗa da taron yanki na Afirka da Latin Amurka, da Asiya-Pacific, bangarorin da ke da muhimmancin manufofin ƙasashen waje da na baya-bayan nan ga Turkiyya.
Kwamitin da zai tattauna batutuwan yankin Balkan zai haɗa da ministocin harkokin wajen ƙasashen Serbia, Montenegro, Bosnia and Herzegovina, da kuma Arewacin Macedonia, tare da wakilin Birtaniya na musamman kan yankin Balkan. Za su tattauna ƙalubale da damarmaki a yankin.
Taron zai kuma tattauna kan Ƙungiyar Haɗin Kan Tattalin Arzikin Bahar Aswad da batutuwan tsaro, tare da ɓangarori biyu kan Eurasia da ƙasashen Turkiyya.
Za a tattauna batun kafa hukumomin Turkiyya da ci gaban da aka samu a ƙarni na 21, tare da inganta haɗin gwiwa tsakanin majalisar a matakin ministoci.
Mevlut Cavusoglu, shugaban tawagar Turkiyya a Majalisar Dokokin NATO zai halarci taron.
Kwamitin Eurasia zai tattauna batutuwan da suka shafi yankin da kuma damar yin haɗin gwiwa a fannin tattalin arziki.
Zai haɗa da shugabannin ƙungiyoyin yanki da wasu wakilan kasashe da ke tattaunawa kan batun "haɗin kai."
"Tubalan Gina Dauwamammen Zaman Lafiya A Gabas Ta Tsakiya"
Za a gudanar da wani zama kan yankin Gabas ta Tsakiya tare da bangarori hudu da za su tattauna batutuwa daban-daban a yankin.
Kwamitin tuntuɓar juna a Zirin Gaza wanda Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya karbi bakunci, zai tattauna kan kokarin da ake na dakatar da batun Falasdinu da kisan kiyashi da ake yi a Gaza, da kuma musayar ra'ayi.
Taron wanda za a gudanar a tsakanin mambobin kungiyar tuntuba, an shirya shi ne ya hada da mataimakin firaministan kasar kuma ministan harkokin wajen kasar Jordan, tare da ministocin harkokin wajen Falasdinu da Masar da Saudiyya.
Kwamitin mai taken Tubalan Gina Dauwamammen Zaman Lafiya Mai Dorewa a Gabas Ta Tsakiya zai kuma yi jawabi kan abubuwan da suka faru a Gaza.
Zai hada da ministocin harkokin wajen kasashen Lebanon da Falasdinu da mataimakin ministan harkokin wajen Bahrain, da mataimakin babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa.
Za a kuma tattauna tsarin ba da tabbacin Turkiyya na samar da mafita ta dindindin ga al'amarin Falasdinawa.
Kwamitin na hudu, wanda ya mai da hankali kan Gabas ta Tsakiya, za a gudanar da shi ne a matakin ƙwararru, tare da hada kan 'yan jarida da masu fasaha daga yankin don tattauna "yadda za a iya samar da wani sabon yanayi a Gabas ta Tsakiya."
Siyasar duniya da tsaro
Bangaren "Siyasa da Tsaro na kasa da kasa" zai gabatar da bangarori da za su tattauna batutuwa daban-daban da suka hada da rawar da "mata" ke takawa a fannin tsaro da diflomasiyya.
Taron mai taken "Mata, Zaman Lafiya, da Tsaro" karkashin jagorancin uwargidan shugaban kasar Emine Erdogan, zai kasance na musamman da kuma babban matsayi.
Za a kuma tattauna batun wariyar launin fata da ƙyamar baƙi da ƙyamar Musulunci da sasantawa a dandalin.
Wani kwamitin da zai tattauna matsalar sauyin yanayi, wanda kuma zai gabatar da matakan magance batun makamashi da samar da abinci, zai samu halartar kasashen Afirka da Gabas ta Tsakiya.
Akwai wani zaman da zai tallafa wa kasashen da ba su ci gaba ba, tare da halartar wakilai daga Bankin Fasaha na Majalisar Dinkin Duniya da Cibiyar Bunkasa Masu Zaman Kansu ta UNDP.
Za kuma a gudanar da wani taron mai taken "Ciniki na kasa da kasa da Haɗin kai, da dogaro da juna," wanda mataimakin shugaban ƙasar Cevdet Yilmaz zai halarta.