Amurka ta yi maraba da kokarin Turkiyya wajen shawo kan Rasha ta koma kan yarjejeniyar hatsi da aka cimma ta Tekun Bahar Aswad, a cewar Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka.
"Muna kan tattaunawa da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Turkiyya, wadanda suke kan gaba wajen ganin tsarin na shirin fitar da hatsi a Tekun Bahar Aswad ya yi aiki yadda ya kamata," in ji mataimakin mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin wajen Amurka Vedant Patel a hirarsa da manema labarai a ranar Talata.
Vedant ya mayar da martani ne ga wata tambayar da aka yi masa kan ganawar da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi da shugaban Rasha Vladimir Putin a birnin Sochi.
"Muna kuma gode wa kawayenmu na NATO da Turkiyya, saboda muhimmiyar rawar da suke takawa a kokarin ganin an dawo da shirin hatsi na Bahar Aswad a kan turba," in ji shi.
Patel ya ce, shawarar da Rasha ta yanke kan dakatar da shigarta cikin shirin samar da hatsi na Tekun Bahar Aswad "ya cutar da al'ummomin da ke fuskantar matsalar karancin abinci a duniya."
Da aka tambaye shi game da rahotannin da ke cewa Amurka na ba da shawarar a mayar da hanyar Kogin Danube a matsayin madadin hanyar da ake bi ta Bahar Aswad, Patel ya ce hakan burin Amurka ne kuma tana fatan Rasha za ta dawo cikin yarjejeniyar hatsin.
"Tabbas muna kan ci gaba da tantancewa da kuma duba wasu hanyoyin da ake da su don tabbatar da cewa jigilar kayayyakin abinci na iya isa wuraren da ya kamata," in ji shi.
"Muna son shirin hatsi na Bahar Aswad ya ci gaba da aiki, domin mun san cewa ya yi aiki a baya," in ji Patel.
"Kuma muna matukar godiya ga Majalisar Dinkin Duniya da takwarorinmu na Turkiyya kan rawar da suka taka a baya wajen cimma wannan yarjejeniya da kuma rawar da suke ci gaba da takawa wajen shawo kan Rasha," a cewar Patel.
Erdogan ya fada a ranar Litinin a yayin dawowarsa daga ziyarar da ya kai birinin Sochi da ke gabar tekun Rasha cewa ya gana da Putin kuma ya yi imanin cewa nan ba da jimawa ba za a cimma “sakamako mai kyau” kan farfado da yarjejeniyar hatsi.
A ranar 17 ga watan Yuli ne Rasha ta dakatar da yarjejeniyar ci gaba da kasancewar cikin shirin fitar da hatsi, wadda Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya suka kulla ta dawo da fitar da hatsi daga tasoshin jiragen ruwa uku da ke Tekun Bahar Aswad da aka dakatar bayan soma yakin Ukraine a watan Fabrairun 2022.
Moscow dai ta sha yin korafin cewa Kasashen Yammacin Duniya ba su cika sharuddansu ba game da fitar da hatsin da Rasha ke yi. Yana mai cewa dakatar da biyan kudade da ayyuka da kuma inshora sun kasance abubuwan da suka janyo cikas a aikin jigilar kayayyaki.