Türkiye's international struggle led by President Recep Tayyip Erdogan is an honourable fight against global injustice, Altun says. / Photo: AA

Darektan sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya ce ya kamata a sabunta ilimin kafofin watsa labarai na dijital don amfani da ƙirƙirarriyar basira a masana'antar.

Da yake jawabi a wajen taron ƙara wa juna sani kan amfani da ƙirƙirarriyar basira da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ta shirya a Ankara ranar Laraba, Altun ya ce: Idan muna son amfani da cin gajiyar ƙirƙirarriyar basira a fannin watsa labarai, dole ne sai mun sabunta ilimin watsa labarai na intanet don sanya ƙirƙirarriyar basira a cikin dabarun da kuma sauƙaƙa shi don amfanin al'umma.

"Muna son inganta ilimin intanet a fannin watsa labarai ta hanyar amfani da sabbin fasahohi tare da sauƙaƙa wa al'umma hanyar amfani da su. Ɗaya daga cikin muhimman matakan da muka ɗauka a wannan bigiren shi ne jajircewarmu a wajen yaƙi da labaran ƙarya.

"Ƙoƙarin da muke yi na yaƙi da labaran ƙarya ya haifar da wayar da kan jama'a kuma ya kawo sabon salo da tsarin ci gaba ga ilimin kafofin watsa labarai na dijital," Altun ya ƙara da cewa.

Ya ce wani ƙarin muhimmin matakin na amfani da ƙirƙirarriyar basira a fannin watsa labarai yana samar da ƙa'idojin amfani da ƙirƙirarriyar basira tare da bayyana fatan cewa zai zamo ɗaya daga cikin sakamakon taron.

Dole ne mu yi aiki tare da sanin cewa fasahohin leƙen asiri suna da alaƙa kai tsaye da tsaron ƙasa. A cikin wannan tsari, ba cibiyoyin gwamnati kaɗai ba, har ma da kamfanoni masu zaman kansu ya kamata su ɗauki nauyinsu,” in ji daraktan sadarwa.

"Mun yi imani, a karkashin jagorancin shugabanmu (Recep Tayyip Erdogan), cewa sabon zamani zai zama ƙarni na sadarwa da dijital. Saboda haka, muna aiki don tabbatar da gaskiya da ingantaccen amfani da bayanan sirri a cikin kafofin watsa labarai don gaskiya."

Samun ƙwarin gwiwar amfani da AI

Don shawo kan ƙalubalen amfani da ƙirƙirarriyar basira a kafofin watsa labarai da kuma amfana daga damar da take bayarwa, Altun ya ce: "Muna buƙatar kiyaye 'yancin ɗan'adam da mulkin ɗan'adam da jagoranci na ɗan'adam da tsarawa, da kuma tantancewa."

"A cikin yanayin amfani da ƙirƙirarriyar basira a kafofin watsa labarai, batun lalata basirar mutane da lalata al'adu wani lamari ne da ya kamata mu samar da dabarun yadda za a tafiyar da su.

"A bayyane yake cewa muna bukatar jajircewa wajen amfani da ƙirƙirarriyar basira a kafofin watsa labarai. Za su dogara ga tarihi da al'adu da ikon ɗan'adam, da kuma dogara ga juna," in ji Altun.

Ya ce tsarin da ke bayan rashin adalci a duniya shi ma yana samar da kuma amfani da fasahar AI, ya ƙara da cewa: “Kamar yadda yake a yanzu, ƙirƙirarriyar basira wata aba ce da ke kara zurfafa rashin adalci a duniya.

"Idan har za mu tattauna tsarin adalci na kafofin watsa labarai a duniya a yau, to a matsayinmu na bil'adama, wajibi ne mu tabbatar da daidaito mai kyau tsakanin adalci da mulki don tabbatar da zaman lafiya da wadata da kwanciyar hankali a duniya."

Ya ƙara da cewa gwagwarmayar ƙasa da ƙasa ta Turkiyya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Recep Tayyip Erdogan, yaƙi ne mai daraja da rashin adalci a duniya.

TRT World