Erdogan ya ce shirin hatsi na Bahar Black ya ba da damar wucewar kusan tan miliyan 33 na hatsi don isa ga masu bukata, tare da hana matsalar abinci ta duniya. Hoto: AA

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Ankara za ta ci gaba da ƙoƙarin samar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine.

"Yayin da muke ci gaba da hadin gwiwa da Ukraine, za mu ci gaba da kokarin kawo ƙarshen yaƙin da wanzar da zaman lafiya cikin adalci bisa shawarwari," in ji Erdogan a ranar Juma'a a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Ukraine Volodymr Zelenskyy, a Istanbul.

Ya ƙara da cewa "Turkiyya a shirye take ta karɓi baƙuncin taron zaman lafiya wanda ita ma Rasha za ta halarta."

Ya bayyana cewa, Turkiyya za ta goyi bayan sake gina ƙasar Ukraine da yaƙi ya ɗaiɗaita.

Shugaban na Turkiyya ya ƙara da cewa: "Shigar da yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci (da Ukraine) da wuri-wuri, babu shakka zai farfaɗo da dangantakarmu da ƙarfi.

A yayin taron manema labarai, Shugaban Ƙasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya gode wa Turkiyya da al'ummar Turkiyya bisa goyon bayan da suka bayar ga 'yancin kan yankin Kiev, da ƴancin kai, yana mai cewa sun samu "sakamakon ayyukan jinƙai."

Hanyar jigilar hatsi ta Bahar Aswad

Kafin taron na hadin gwiwa, shugabannin biyu sun gana a ofishin Dolmabahce da ke Istanbul.

Zelenskyy ya faɗa a cikin wata sanarwa a farkon taron cewa yana godiya da goyon bayan Turkiyya.

Ya ce, yana da sha'awar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, da kare zirga-zirgar jiragen ruwa a cikin muhimman hanyoyin jigilar kayayyaki a Tekun Bahar Aswad, da kuma ganin Ukraine ta yi aiki tare da kamfanonin tsaron Turkiyya.

Ya ƙara da cewa suna kuma bukatar taimakon Turkiyya wajen sako fursunonin yakin Ukraine da kuma "dukkan mutanenmu, ciki har da 'yan Tatar na Crimea, wadanda Rasha ke riƙe da su."

A Istanbul, Zelenskyy kuma zai ziyarci wuraren ajiyar jiragen ruwa inda kamfanonin Turkiyya ke gina wa sojojin ruwa na Ukraine guda biyu, a cewar ofishinsa.

TRT World