Yusuf Abdullahi: Dan wasan da ya taimaka wa Kano Pillars ta lallasa Gombe United a gida

Yusuf Abdullahi: Dan wasan da ya taimaka wa Kano Pillars ta lallasa Gombe United a gida

Dan wasan bai taba zura ƙwallo a raga ba a gasar Firimiyar Nijeriya kafin karawar Gombe United da Kano Pillars.
Yusuf Abdullahi ne ya yi ta ruwan kwallo a ragar Gombe United. Hoto/Twitter/NPFL

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta yi wa Gombe United dukan kawo-wuƙa da ci 5-2 a karawar Gasar Firimiyar Nijeriya da suka yi a filin wasan Unguwar Pantami da ke garin Gombe ranar Lahadi.

Dan wasan gaban Masu Gida mai shekara 18, Yusuf Abdullahi, ne ya zura ƙwallaye biyar ɗin a ragar Gombe United.

Yusuf dai ya fara zura ƙwallaye a ragar Gombe United a minti 11 da minti 14 da fara wasa, yayin da Sadiq Shuaibu ya farke wa Gombe United ƙwallo daya a minti na 17.

Sai dai kuma Yusuf bai ƙyale Gwambawa haka ba domin ya kara zura ƙwallaye a ragarsu a minti 33 da kuma minti 45.

Kwallon da Ahmed Jimoh ya farke wa Gombe United minti 45 bayan an fara wasa ba ta iya ceto Gombe United ba, domin Yusuf ya ƙara musu ƙwallo daya minti 60 da fara wasa.

Yusuf ya ce yana maraba da gayyata zuwa tawagar kwallon kafar Nijeriya. Hoto/Twitter/NPFL

Kocin Kano Pillars, Abdullahi Maikaba ya taya Yusuf Abdullahi murnar kwallo na farko da ya zura a raga a kakar bana.

“Na sha fada masa cewa ƙwallonsa ta farko na da muhimmanci. Idan ya samu ya ci ƙwallonsa ta farko, zai samu ƙarfin gwiwar ƙara cin ƙwallaye,” in ji Maikaba.

“Na yi murnar ganin cewa ƙwallonsa ta farko ta ƙarfafa masa gwiwa wajen ƙara zura ƙwallaye hudu a raga,” kamar yadda Maikaba ya bayyana.

Yusuf Abdullahi ya bayyana murnarsa ga irin nasarar da ya samu a wasan.

Dan wasan na Pillars ya ce zai yi na’am idan aka gayyace shi tawagar ƙwallon kafar Nijeriya.

TRT Afrika