Daga Charles Mgbolu
Yayin da ake shirye-shiryen fara wasa a yammacin ranar Laraba a filin wasa na El Abdi a kasar Maroko, ’yan wasan Ethiopia da Saliyo da ke shirin fafatawa a wani wasa mai muhimmanci na neman gurbin Gasar Kofin Duniya ta 2026, ba su da masaniya kan yadda yanayin zai canja.
Minti biyar bayan fara wasa, sai aka fara ganin hazo ko da yake hakan bai sa an tsayar da wasan ba, inda kowane bangare yake neman zura kwallo a ragar abokin karawarsa.
Sannan lokacin da wasan ya kai hutun rabin lokaci, akwai alamun da ke nuna cewa za a samu matsala.
Daga nan ne sai hazo ya fara sauka a filin wasan, inda Hukumar Kwallon Kafar Ethiopia ta fara wallafa hotunan ’yan wasa a shafukan sada zumunta wadanda ba sa gani sosai.
Yayin da ake hutun rabin lokaci, ’yan wasa sun sake koma wa dakin canja kaya, sannan an hango jami’an hukumar FIFA da alkalan wasa suna kokarin yanke shawara kan yadda za a ci gaba da wasan.
Masu kwallon wasan ta talabijin sun rika nuna damuwa lokacin da aka kawo karshen minti 15 na hutun rabin lokaci, amma ’yan wasa ba su koma filin wasan ba.
Mutane sun ji dadi a shafukan sada zumunta bayan da aka dawo wasan bayan sa’a daya.
“Labari mai dadi! An dawo wasan…Ba a gani tar-tar!” kamar yadda wani mai son kwallon kafa @negussu ya wallafa ashafin X.
’Yan wasa ba su ce sakamakon wasan yana da alaka da yanayin ba./ Hoto Ethiopia Football Federation
Alkalan wasa sun tsayar da wasan sau biyiu bayan da aka dawo hutun rabin lokaci, sannan a karshen wasan an kara minti 15 na cikon lokaci.
’Yan wasan daga duka bangarorin biyu sun yi magana bayan gama wasan wanda aka tashi kunnen doki 0-0, sai dai ba su ce yanayi ya yi tasiri a kan sakamakon wasan ba.
Saliyo za ta kara da Masar a ranar 19 ga watan Nuwamban, yayin da Ethiopia za ta kara da Burkina Faso a ranar 21 ga watan Nuwamba.