Mbappe ya ci kwallaye uku a wasan./Hoto:Reuters

Faransa ta samu nasara mafi girma a wasan cancantar zuwa Gasar Zakarun Turai bayan ta doke tawagar Gibraltar mai ‘yan wasa 10 da ci 14-0 ranar Asabar.

Kylian Mbappe ya zura kwallo uku rigis yayin da Warren Zaire-Emery ya ci kwallo a wasansa na farko.

Faransa ta kawar da tahirin da Jamus ta kafa inda ta ci San Marino 13-0 a 2006 a wasansu mafi girma a tarihi a fagen kwallon kafar duniya. Kazalika wannan ne karo na farko da wata tawagar Turai ta ci kwallo 14 a wasan cancantar zuwa Gasar cin Kofin Duniya da kuma Gasar cancantar shiga Gasar Zakarun Turai.

Marcus Thuram, Zaire-Emery, Mbappe, Jonathan Clauss, Kingsley Coman da Youssouf Fofana sun ci kwallo kafin tafiya hutun rabin lokaci a wasan na Rukunin B bayan Faransa ta zura wa kanta kwallo minti uku da soma wasa.

A yayin da Faransa ta tabbatar da matsayinta na jagora a Rukunin, Deschamps ya mika wa Zaire-Emery mai shekara 17 kwallo inda ya zura ta, inda ya zama dan wasan Faransa na farko mafi karancin shekaru tun 1914.

Ya kasance dan wasan kasar mafi karancin shekaru tun wancan zamanin inda ya ci kwallo a minti na 16, ko da yake Ethan Santos ya daki kaurinsa.

An kori dan wasan na Gibraltar daga wasa yayin da shi ma Zaire-Emery aka dauke shi daga wasan.

Adrien Rabiot da Coman sun zura kwallaye sannan Ousmane Dembele ya zura tasa kwallon inda wasan ya kasance 10-0. Sai kuma Mbappe ya kara zura karin kwallo biyu, lamarin da ya sa wasa ya koma 12-0.

Wasan ya koma 14-0 bayan an saka Olivier Giroud wanda ya zura kwallo biyu, kuma kwallo ta 56 da ya ci wa kasarsa.

Faransa, wadda ta yi nasara a dukkan wasanninta bakwai na rukini, za ta fafata da Girka ranar Talata a wasan karshe.

"Za mu ji dadin abin da muka yi yau da daddare, ba za mu je Girka don yin sharholiya ba. Za mu sake zura kwallaye," in ji Deschamps.

Reuters