Kazalika hatsarin ya sa dan wasan ya samu matsala da kwakwalwarsa./Hoto:Reuters

An sallami golan Paris Saint-Germain Sergio Rico daga asibiti ranar Juma'a, watanni uku bayan an kwantar da shi sakamakon hatsarin da ya samu wanda ya jefa shi cikin halin dogon suma.

Kazalika hatsarin ya sa dan wasan ya samu matsala da kwakwalwarsa.

An kwantar da dan wasan na kasar Sifaniya mai shekara 29 a asibitin Virgen del Rocio da ke Seville tun ranar 28 ga watan Mayu bayan ya yi hatsari sakamakon wasan sukuwar dawaki.

"Tabbas, kwakwalwa tana da basira kuma takan goge irin wadannan abubuwa da suka faru -- zancen gaskiya shi ne... na ji kawai ina mafarki ne, sai na tashi a nan asibitin, kuma ina godiya ga Allah, yanzu ina matukar farin ciki," in ji Rico.

"Ina fatan warkewa a hankali nan ba da jimawa ba sannan na koma kwallon kafa."

Kocin PSG Luis Enrique ya yi wa Rico fatan alheri.

"In so na mika sako ga Sergio Rico, wanda aka sallama daga asibiti yau, kuma mu a nan kungiyarsa, muna fata ya samu sauki, ya dawo bakin aiki -- muna mika dukkan goyon bayan kungiyar nan gare shi da iyalansa," a cewarsa.

An sallami dan wasan daga sashen bayar da kulawar gaggawa ranar 5 ga watan Yuli bayan ya farrfado daga dogon suman da ya yi.

Kwana biyar bayan haka, Rico ya wallafa sako a shafinsa na sada zumunta domin shaida wa mutane halin da yake ciki.

"Ina mika godiya ga kowa bisa kaunar da aka nuna mini sakamakon mawuyacin halin da nake ciki," kamar yadda Rico ya wallafa a Instagram.

TRT Afrika