Kocin Barcelona Xavi Hernandez ya cimma matsaya da kulob din da yake jagoranta inda zai ci gaba da zama a can har zuwa 2025.
Ana sa ran sanar da abin da yarjejeniyar da Xavi ya kulla da Barcelona kafin karshen mako mai zuwa idan Xavi din ya tattauna da daraktan wasanni Deco a kwanaki masu zuwa.
Xavi ya karbi jagorancin Barcelona a 2021 bayan Ronald Koeman ya bar kulob din.
A lokacin da ya karbi jagorancin kulob din, ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara uku wadda za ta kawo karshe a kakar 2023/2024.
Sai dai kocin mai shekara 43 a halin yanzu ya amince ya kara tsawaita zamansa a kulob din na karin wasu shekaru kamar yadda jaridar wasani ta Mundo Deportivo ta kasar Sifaniya ta ruwaito.
Duk da cewa wakilin Xavi Fernando Solanas shi ya assasa tattaunawa da tsohon daraktan wasanni na Barcelona Mateu Alemany a lokacin kaka, abin da kulob din yake so a lokacin da aka bude cinikin ‘yan wasa shi ne ya kara gina ‘yan wasansa.
Sai dai a halin yanzu da aka rufe kasuwar ‘yan wasan, kulob din ya mayar da hankali kan sabunta kwantiragin Xavi.
Xavi ya soma buga wasa a kulob din yara na Barcelona tun daga 1991 inda daga nan ya yi ta wasa har zuwa babbar kungiyar ta Barcelona.
A 2015 ya bar kungiyar zuwa Al Sadd ta kasar Qatar inda a nan ya yi ritaya daga buga wasanni a 2019.
Daga nan ne ya soma aikin horas da ’yan wasa a kulob din na Al Sadd inda a 2021 kuma ya koma kulob dinsa na asali wato Barcelona.