Xabi Alonso, wande ke jagorantar ƙungiyar Bayer Leverkusen ta Jamus ya ƙi amincewa ya bar kulob ɗin da yake jagoranta, wanda a kakar bana ya buga wasanni 38 ba tare da yin rashin nasara ba.
Kocin mai farin jini, ya sanar da wannan hukuncin ne ranar Juma'ar nan duk da cewa cikin ƙungiyoyin da ke neman sa har da waɗanda ya buga wa wasa, wato Liverpool ta Ingila da Bayern Munich ta Jamus.
Alonso ya yanke hukuncin cigaba da zama a kulob ɗinsa da yake dab da lashe kofin gasar Bundesliga ta Jamus, har zuwa kakar baɗi.
Kocin wanda ɗan asalin Sifaniya ne, ya samu farin jini musamman wajen manyan kulob ɗin biyu, sakamakon cewa masu horar da su za su yi murabus daga jagorantar su a ƙarshen kakar bana.
Tuni Liverpool ta sanar da tafiyar kocinta na yanzu, Jorgen Klopp, haka ita ma Bayern Munich za ta rabu da kocinta da zarar an kammala kakar ta bana.
Leverkusen ƙarƙashin Xabi Alonso tana dab da ɗaukar kofin Bundesliga a karon farko a tarihin ƙungiyar. A wannan shekarar sun yi zarra wajen rashin shan kaye a wasannin da suka buga a duka gasannin da suke ciki.
Alonso ya sanar wa taron manema labarai cewa ba zai amshi tayin horar da Bayern Munich ba, duk da sun rigaya ambata shi a matsayin wanda suke fatan miƙa wa ragamar ƙungiyar.
Tun ranar Alhamis ne alamu suka nuna cewa Liverpool ta haƙura da neman Alonso, wanda tsohon ɗan wasanta ne a zamanin da yake buga ƙwallo, domin ya maye gurbin kocinta Jurgen Klopp.
Da yake magana da 'yan jarida, Alonso ya ce, "Mun ji raɗe-raɗi daban-daban game da makomarta. Ina so na yi amfani da hutun nan don yin tunani da yanke hukunci. A makon baya na sanar da kulob ɗina cewa zan ci gaba da zama koci".
"Aikina a nan bai ƙare ba. Ina ganin nan ne ya dace da ni na zauna, kuma na inganta aikina na horar da 'yan ƙwallo."
Alonso yana da shekaru 42 a duniya, kuma yana da burin cin kofuna uku a bana, inda Bayer Leverkusen take da fifikon maki 10 a teburin Bundesliga, kuma ta kai matakin ƙarshe na gasannin DFB-Pokal da kuma Europa League.
Tun da hankalin Leverkusen ya kwanta yanzu, ƙungiyar tana fatan ƙarasa aikinta inda take fatan nasara a wasanta da Hoffenheim ranar Asabar, kafin ta koma kan wasan dab da na ƙarshe a kofin Dusseldorf a tsakiyar mako.