Liverpool ta kara samun maki a gasar ta firimiya. Hoto/Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta lallasa Wolverhampton Wanderers da ci 3-1 a Gasar Firimiya.

Wannan shi ne karo na uku da kungiyar ta ci wasa a cikin wasanni biyar da ta buga.

Kunigyar ta Wolves ta rike Liverpool gagagam a zagaye na farko kafin a tafi hutun rabin lokaci inda dan wasanta Hwang Hee-chan ya soma zura kwallo a ragar Liverpool.

Sai dai bayan da aka dawo hutun rabin lokaci, ‘yan wasan na Liverpool sun nuna zafin nama inda Cody Gakpo ya rama ci dayan da aka musu bayan Mohamed Salah ya tura masa kwallon.

A lokacin da ake cikin minti na 85, sai Andy Robertson wanda wannan shi ne wasansa na 200 daidai a gasar Firimiya League ya zura kwallo ta biyu a ragar Wolves.

Sai dai ci na ukun da Liverpool ta yi ya kasance mai ban haushi sakamakon abokan karawar tasu sun ci kansu ne bayan Harvey Elliott ya durka kwallo sai ta taba jikin Hugo Bueno ta shige raga.

Wannan cin da Liverpool ta yi ya sa ta kara sama da maki daya a kan teburin gasar Firimiya

TRT Afrika