Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya yi magana kan batun da ke yawo cewa shahararren dan wasan kungiyar, Mohamed Salah zai koma wasa Saudiyya.
A ranar Alhamis wasu kafafen yada labarai a Birtaniya suka ruwaito cewa kungiyar Al-Ittihad tana son sayen dan wasan mai shekara 31, wanda yake da sauran shekara biyu a kwantiraginsa da Liverpool.
"Babu wani abu da za mu ce daga bangarenmu. Mo Salah dan wasan Liverpool ne, saboda abin da muke yi. Babu wata magana. Idan ma akwai, to za mu ce a'a," in ji Klopp.
Wakilin Salah Ramy Abbas Issa a wannan watan ya ce dan wasan gaban Masar din yana tare da Liverpool.
Salah, wanda ya koma Liverpool daga Fiorentina a 2017, ya zura wa kungiyar kwallaye 187 a wasanni 308, kuma shi ne dan wasan da ya fi karbar albashi a tarihin kungiyar.