Keftin din kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila Harry Kane ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara hudu da Bayern Munich har zuwa 2027, kamar yadda kungiyar ta Bayern ta sanar a ranar Asabar.
Kungiyoyin biyu sun yi yarjejeniya kan tsabaragen kudi da za a iya cewa an kafa tarihi a gasar Bundesliga wato euro miliyan 100, kwatankwacin dala miliyan 110 kenan kan dan wasan mai shekara 30 wanda yake da sauran shekara daya a kwantiraginsa da Tottenham.
“Na ji dadi matuka da na zama dan FC Bayern a yanzu,” kamar yadda Kane ya bayyana a sanarwar da kulob din ya fitar.
Zakarun na kasar Jamus na cikin matsananciyar damuwa inda suke ta neman dan wasan gaba, bayan sun sha gwagwarmayar cike gurbin Robert Lewandowski a kakar da ta gabata.
Kane ya ci kwallaye 280 a wasanni 435 da ya buga a Tottenham kuma shi ne ya fi kowa cin kwallaye a Ingila inda ya ci kwallaye 58 a wasannin kasa da kasa.
Har yanzu dai bai ci kofi a wata babbar gasa ba a kulob dinsa ko kuma a matakin kasa.