Mai tsaron gidan Manchester United Andre Onana ya karbi kuskurensa bayan sun yi rashin nasara a hannun Bayern Munich da ci 4-3 a wasan Rukunin A na Gasar Zakarun Turai.
Kuskuren da Onana ya yi kafin a tafi hutun rabin lokaci ya sa Leroy samun nasarar jefa kwallo a ragar United a minti na 28.
A wajen yadi na 18 ne Sane ya buga shot zuwa bangaren dama na raga. Sai kwallon ta subuce a hannun Onana, inda yawancin magoya bayan Manchester United suke cewa bai kamata ya bari kwallon ta shiga raga ba.
"Rashin nasara abu ne mara dadi. Mun fara wasa mai kyau daga farkon wasan. Amma bayan da na yi kuskure, sai wasan ya bar hannunmu. Mawuyacin hali ne a gare mu, musamman ma a gare ni, saboda ni ne na jawo wa kungiyar matsala," kamar yadda Onana ya bayyana yayin da yake zantawa da manema labarai bayan wasan a ranar Laraba.
"Tawagarmu tana da kyau sosai. Ya kamata mu tari gaba," in ji shi.
A karshe, an tashi wasa ne da ci 4-3 wanda za a iya cewa Manchester United din ta dan tabuka wani abu.
An zura masa kwallaye da yawa a raga
"Eh, kwallon farko (laifina ne). Na fahimci cewa mun yi rashin nasara ne saboda ni," in ji Onana.
An zura wa golan kasar Kamarun kwallaye 14 a kakar bana – kwallaye 10 a wasanni biyar na Gasar Firimiya Lig da hudu a wasan farko a Gasar Zakarun Turai.
Saboda yadda kwallaye da yawa suka shiga ragarsa, dan wasan mai shekara 27, ya ce "bai fara wasa da kafar dama ba" a Manchester United.
"Akwai jan aiki sosai a gabana (don na gamsar da magoya bayan Manchester United). Batun gaskiya, wasanni na farko a United ba su yi kyau ba, ba abin da nake son yi ba kenan. Mu babbar kungiya ce, muna so mu yi nasara a duka wasanni. Ya kamata mu kasance tare, ya dace mu ci gaba da yin aiki tukuru kamar yadda muke yi," kamar yadda ya ce a ranar Laraba.
Onana ya maye gurbin Daivid de Gea wanda ya dade a Manchester United.
Onana ya koma United ne daga Inter Milan a kan fam miliyan 43.8 (dala miliyan 57.3 kenan).