Madugun Inter a yau, Eden Dzeko, ya taimaka wa Man City wajen lashe kofin gasar Firimiya a karon farko a kakar 2011-12. Shin a yau zai iya hana City lashe kofuna uku cikin kaka daya, a karon farko a tarihinta? /Hoto: Reuters

A yayin da Inter Milan za ta kara da Manchester City mai neman kofi na uku cikin kakar bana, dan wasan da City ta sayar shekaru takwas da suka wuce zai iya kasancewa madugun Inter Milan a wannan karon.

Kwallayen Edin Dzeko dai sun taba taimaka wa City ta lashe Kofin Gasar Firimiya har sau biyu, da kofin FA da kuma kofin EFL. Ko tsohon dan wasan kulob din City zai nemi daukar fansa ne a yanzu?

Wannan ya sa wasu na ganin idan akwai wanda zai iya kawo cikas ga kungiyar da Pep Guardiola ke jagoranta, kuma ya gagari kowa a wasan karshe da za a buga a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

'Yana taka rawar gani a ko ta ina'

A cikin minti takwas kacal ne Inter Milan ta zura kwallo a ragar AC Milan, a karawarsu ta farko a matakin daf da na karshe a Gasar Zakarun Turai ta wannan kakar.

Hakan Calhanoglu ne ya bugo kwallon, sai kuma dan kasar Bosniya, Eden Dzeko, ya buga ta da karfi da kafarsa ta hagu zuwa cikin ragar AC Milan.

Shin dan wasan da City ta sayar a kakar 2016 zai iya hana ta lashe gasar zakarun Turai a wannan shekara? /Hoto: Reuters

Masharhanta na ganin ba kowa ne zai iya zura irin wannan kwallon a raga ba, saboda kwallon tana bayansa ne, amma ya iya danna ta cikin raga ta sama.

A wasan matakin daf da na karshe na kofin zakarun Turai na bana ma, kwallon da Dzeko ya zura ita ce ta farko da suka ci, inda aka tashi wasan Inter tana da kwallaye uku, AC kuma tana nema.

Masharhanta suna ganin dan wasan yana da basira da kuma baiwa na iya urza leda.

Babu Aguero babu Dzeko

Duk da cewa a yanzu da ya kai shekara 38 yana zura kwallo a raga, magoya bayan City za su cigaba da tunawa da Dzeko ne kan rawar da ya taka sanda yana can.

Yayin da Queens Park Rangers ke gaban City da ci 2-1 a karshen kakar 2011-12, Dzeko ya tashi sama kuma ya yi amfani da kai wajen tura kwallo a raga, cikin minti na 92 da fara wasa, lamarin da ya sa wasan ya koma 2-2.

Jim kadan kuma sai CIty ta samu ta zura kwalon da ya kai ta ga nasara, wanda Sergio Aguero ya zura ci mata. City ta lashe gasar Firimiyarta ta farko ta dalilin wannan kwallaye na Dzeko da Aguero.

A ranar Asabar Dzeko zai samu damar daukar kofin gasar Zakarun Turai/Hoto:Reuters

Daga Sarajevo zuwa Serie A

Eden Dzeko, wanda ya girma a Sarajevo a lokacin yakin Bosniya, ya fara wasansa a shekarar 2003 da kungiyar Zeljeznicar.

A lokacin dan wasan tsakiya ne, kuma ya koma kungiyar FK Teplice ta jamhuriyar Czech daga nan kuma ya koma Wolfsburg ta Felix Magath, a shekarar 2007.

Dan wasan da aka yi wa lakabi da lu’ul’un Bosniya ya zura kwallaye 85 a raga cikin wasanni 142 da ya buga wa Wolfsburg, kuma ya taimaka wa kungiyar ta Jamus lashe kofin gasar Bundesliga a karon farko a shekarar 2009.

Duk da cewa shi ne dan wasa na 13 da ya fi iya murza leda a jadawalin Ballon d'Or a shekarar 2009, har yanzu dan wasan na zura kwallo a raga bayan wajen shekara 14.

A watan Janairun 2011, ya koma taka leda a Man City kan yarjejeniya ta fam miliyan 27, a wancan lokacin Ronaldinho ne kawai dan wasan da wata kungiyar gasar Firimiya ta kashe kudin da ya fi haka a kansa (fam miliyan 32.5).

Duk da cewa dan wasan ya dade yana zura kwallo a raga, har yanzu yana iya zura muhimman kwallaye a raga/Hoto:Reuters

Bayan ya taimaka wa City lashe kofin gasar Firimiya sau biyu, Dzeko ya koma Roma, daga farko a matsayin dan wasan aro, kafin daga baya ya koma na dindindin a shekarar 2015.

Ya kasance dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a gasar Serie A a kakar 2016-17, kafin ya koma Inter, bayan shekara shida, inda ya dauki kofin Coppa Italia sau biyu cikin kaka biyun da suka wuce.

Sai dai tambayar da ake yi yanzu shi ne ko zai iya taimaka wa Inter karya lagon Man City a wasan karshen gasar Zakarun Turai da za su yi a Istanbul ranar Asabar?

TRT Afrika da abokan hulda