Manchester City ta kammala kakar wasan bana da kofuna uku a cikin jakarta inda a yau ta dauki Kofin Zakarun Turai bayan ta doke Inter Milan da ci 1-0.
Sun buga wasan ne a filin Olympic na Atuturk da ke Istanbul.
Tuni kungiyar ta lashe kofuna biyu - na Gasar Firimiya ta Ingila da Gasar FA, kuma hakan na nufin ta zama kungiyar Turai ta biyu da ta lashe kofuna uku a kakar wasa daya - Manchester United ta kafa wannan tarihi a 1999.
Kazalika wannan bajinta ta sa Pep Guardiola ya jaddada matsayinsa na zama daya daga cikin koci mafi shahara inda ya ci kofinsa na uku na Zakarun Turai bayan ya lashe biyu a Barcelona, na karshe shi ne wanda ya dauka a 2011.
'Yan wasan na Guardiola sun yi gumurzu sosai da 'yan wasan Inter Milan, wadanda suka nuna matukar hazaka, sai dai a minti na 68 Rodri ya zura kwallon da ta ba su nasara.
City ta yi nasara ne duk da cewa zakakurin dan wasan tsakiyarta Kevin De Bruyne ya ji rauni kafin a tafi hutun rabin lokaci lamarin da ya sa aka cire shi daga wasan.